Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ireland Ta Ce Za Ta Shiga Tsakani A Batun Zargin Kisan Kiyashi Da Afirka Ta Kudu Ke Yi Wa Isra’ila


Ministan harkokin wajen kasar Ireland Micheal Martin
Ministan harkokin wajen kasar Ireland Micheal Martin

Jiya Laraba kasar Ireland ta ce za ta shiga tsakani a karar Isira’ila da Afurka Ta Kudu ta yi kan zargin kisan kiyashi, a wani mataki na nuna alama mai karfi kan damuwarta game da aika-aikar Isra'ila a Gaza tun ranar 7 ga Oktoba.

Da yake sanar da matakin, ministan harkokin wajen kasar Micheal Martin ya ce yayin da kotun duniya ta yanke hukuncin ko ana aikata kisan kiyashi ko a’a, yana so ya bayyana cewa harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba da kuma abin da ke faruwa a Gaza a yanzu "ya nuna cin zarafi ne a fili wanda ya ta ke dokokin jin kai na kasa da kasa."

"Yin garkuwa da mutane, da hana kai agajin jin kai ga farar hula, da kai hari kan fararen hula da kayayyakin more rayuwa, yin amfani da makamai masu fashewa a wuraren da jama'a ke da yawa, da kuma hukunci na gama-gari, "in ji Martin a cikin wata sanarwa.

"Abubuwan ba su da iyaka, dole a tsaida shi haka, ra'ayoyin kasashen duniya a bayyanai yake a fili. Ya isa haka."

A cikin watan Janairu ne kotun kasa da kasa da aka fi sani da kotun duniya ta umurci Isra’ila da ta guji duk wani abu da zai iya zama kisan kare dangi da kuma tabbatar da cewa sojojinta ba su aikata kisan kare dange kan Falasdinawa ba, bayan da Afirka ta Kudu ta zargi Isra’ila da aikata kisan kare dangi a Gaza.

Isra'ila da kawayenta na Yamma sun bayyana zargin a matsayin mara tushe. Hukuncin karshe a shari'ar ICJ ta Afirka ta Kudu a birnin Hague na iya daukar shekaru.

Israel Palestinians World Court Genocide Defense
Israel Palestinians World Court Genocide Defense

Martin bai bayyana irin nau'i na shiga tsakani ba ko kuma zayyana duk wata hujja da Ireland ke shirin yi don ci gaba ba, amma ya kara da cewa an yanke matakin ne biyo bayan nazarin doka da manufofi da tuntubar wasu abokan hulda da suka hada da Afirka ta Kudu.

Ofishin Martin ya ce irin wannan shiga batu ba na goyon bayan wani bangare ba ne a takaddamar, amma shiga tsakanin zai kasance wata dama ce ga Ireland ta gabatar da irin nata fahimtar kan daya ko fiye da haka na tanade-tanaden kan batun Kisan kiyashi a wannan shari’ar.

Harin da Hamas ta jagoranci kaiwa ya yi sanadin mutuwar mutane 1,200 tare da garkuwa da wasu sama da 250 kamar yadda kididdigar Isra'ila ta nuna. Tun daga wannan lokacin, hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza ya kashe fiye da mutane 32,000, a cewar hukumomin lafiya na Hamas a Gaza.

Kasar Ireland wadda ta dade tana fafutukar kare hakkin Falasdinu, a makon jiya ta bi sahun Spain da Malta da kuma Slovenia wajen daukar matakin farko na amincewa da batun zama kasa da Falasdinawan suka ayyana a yammacin gabar kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye da kuma yankin Zirin Gaza.

Isra'ila ta shaida wa kasashen cewa shirin nasu ya zama tamkar "ba da lada ne ga ta'addanci" wanda zai rage damar yin shawarwarin warware rikicin da ke tsakanin kasashe makwabtan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG