Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afirka Ta Kudu Ta Bukaci Kotun Duniya Ta Gaggauta Yin Bincike Kan Harin Da Isra'ila Ta Kai Kan Rafah A Shari'ar Kisan Kiyashi Da Ake Kan Yi


Israel Palestinians World Court Genocide Defense
Israel Palestinians World Court Genocide Defense

"Isra'ila ta yi imanin cewa tana da ikon yin yadda ta ga dama," in ji ministan harkokin wajen kasar Naledi Pandor.

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta fada jiya Talata cewa ta mika bukatar gaggawa ga kotun kasa da kasa ta Majalisar Dinkin Duniya domin duba ko hare-haren da sojojin Isra'ila ke kaiwa a kudancin Gaza da ke birnin Rafah sun saba wa umarnin wucin gadi da kotun ta yanke a watan jiya a shari'a zargin kisan kiyashi.

Afirka ta Kudu ta ce ta bukaci kotun da ta auna ko harin da Isra'ila ta kai a Rafah, da kuma aniyarta ta kaddamar da farmaki ta kasa kan birnin da Falasdinawa miliyan 1.4 ke fakewa ciki, ya saba wa Kudurin Majalisar Dinkin Duniya kan kisan kare dangi da kuma umarnin farko da kotun ta bayar a watan jiya a wata shari’ar da aka zargi Isra'ila da kisan kare dangi.

Rafah na kan iyaka da kasar Masar, wadda ta yi gargadin cewa duk wani farmaki kan birnin da ke dauke da fiye da rabin al'ummar Gaza zai janyo bala'i.

World Court Genocide Explainer
World Court Genocide Explainer

A cikin wata sanarwa da gwamnatin Afirka ta Kudu ta fitar ta ce Rafah ita ce mafaka ta karshe ga mutanen da suka tsira a Gaza. Ta bukaci babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya da ta duba yiwuwar amfani da karfinta wajen fitar da karin umarnin wuccin gadi ga Isra’ila da ta dakatar da kashe-kashen da ake yi a can.

Tun dama Afirka ta Kudu na zargin Isra'ila da aikata kisan kiyashi kan al'ummar Falasdinu a yakin da take yi da kungiyar Hamas a Gaza inda ta shigar da kara a gaban kotun duniya a watan Disamba. Hukuncin zargin kisan kare dangi na iya daukar shekaru.

A cikin sabon takardar da ta shigar, gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce "ta damu matuka cewa harin da ba a taba ganin irinsa ba na sojojin kan Rafah, kamar yadda kasar Isra'ila ta sanar, ya riga ya kai ga haifar da mummunar kisa, cutarwa da barna."

Afirka ta Kudu ta ce ta na neman a magance lamarin cikin gaggawa "bisa la'akari da yawan mace-macen yau da kullun a Gaza."

Da daren ranar Talata, kotu ta tabbatar a cikin wani sako ta kafar X, wanda a baya a ke kira Twitter, cewa ta karbi sabuwar bukatar ta Afirka ta Kudu. Ba ta yi karin bayani ba. Idan kotu ta yanke shawarar sake zaman sauraron kara kan bukatar karin matakan wucin gadi, za a iya kaiwa makonni kafin ta yanke hukunci.

Banjamin Netanyahu
Banjamin Netanyahu

Isra'ila ta musanta aikata kisan kiyashi a Gaza kuma ta ce tana yin duk mai yiwuwa don ganin ta kare fararen hula kuma kuma kungiyar Hamas ce kawai ta ke kai wa hari. Ta ce dabarar da Hamas ke yi ta shigar da fararen hula a yankunan farar hula ya sa da wuya a kauce wa hasarar rayukan fararen hula.

"Isra'ila ta yi imanin cewa tana da ikon yin yadda ta ga dama," in ji ministan harkokin wajen kasar Naledi Pandor.

Hare-haren na Isra'ila sun yi barna a Gaza, inda aka kashe sama da mutane 28,000, sama da kashi 70% mata ne da yara kanana, a cewar jami'an kiwon lafiya na yankin da ke karkashin ikon Hamas. Kusan kashi 80% na mutanen sun rasa matsugunansu kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce wani bala'in jin kai ya jefa sama da kashi daya bisa hudu na Falasdinawa a Gaza cikin matsanacin yunwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG