Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Fara Sauraran Karar Da Aka Shigar Da Isra’ila Kan Kisan Kiyashi A Gaza


Kotun Kasa da Kasa
Kotun Kasa da Kasa

Alkalai a Kotun Kasa da Kasa, sun fara sauraron ba’asi na tsawon kwanaki biyu daga yau Alhamis, a wata karar da kasar Afirka Ta Kudu ta shigar, ta tuhumar Isra’ila da aikata kisan kiyashi a yakin da ta ke yi a Gaza.

Afirka Ta Kudu na bukatar kotun ta bayar da umurnin dakatar da yakin da Isra’ila ke yi a Gaza, inda Isira’ilar ta ke cewa so ta ke ta kawo karshen kungiyar mayakan Hamas, saboda harin ta’addancin da ta kai ranar 7 ga watan Oktoban bara a kudancin Isira’ila.

A takardar shigar da karar, Afirka Ta Kudu ta ce ta na son kotun ta tuhumi Isira’ila da laifin saba ma Dokar Hana Kisan Kiyahsi, ta kuma “tabbatar da cikakkiyar kariya ga Falasdinawan Gaza, wadanda ke ci gaba da fama, da ke kuma fuskantar hadarin ci gaba da kisan kiyashin.”

Isira’ila dai ta yi watsi da zargin da cewa ba shi da tushe balle makama.

Firai Ministan Isira’ila Benjamin Netanyahu ya fada da yammacin ranar Laraba cewa sojojin Isira’ila na yin duk mai yiyuwa don ganin an rage asarar rasa rayukan fararen hula, kuma ya zargi mayakan Hamas da yin amfani da fararen hula a matsayin garkuwa.

Netanyahu ya ce “Isra’ila tana yakar ‘yan ta’addar Hamas ne, ba al’ummar Falasdinawa ba, kuma muna yin hakan ne bisa bin dokokin kasa da kasa.”

Amurka, wacce ta bukaci Isra’ila da ta kara kaimi wajen kare fararen hula a Gaza, yayin da kuma take marawa yakin da Isira’ila ke yi kan Hamas, ta kuma nuna rashin amincewa da zargin kasar Afirka ta Kudu ke yi mata.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, a ranar Talata ya yi watsi da karar a matsayin “mara inganci.”

Ya ce “abin takaici ne, ganin yadda wadanda ke kai wa Isra’ila hari, Hamas da Hezbollah da Houthi da kuma mai goyon bayansu Iran, ke ci gaba da yin kira da a kawar da Isira’ila da kuma kashe Yahudawa da yawa.”

Hamas ta kashe kimanin mutane 1,200 a harin da ta kai a watan Oktoban bara a Isra’ila tare da kame mutane 240 da aka yi garkuwa da su, wadanda aka sako kusan rabinsu.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza da Hamas ke iko da ita, ta ce harin da Isira’ila ta kai ya kashe Falasdinawa sama da 23,000, yayin da mafi yawancin Gaza ya zama baraguzai kuma kashi 85 cikin 100 na al’ummarta miliyan 2.3 sun rasa matsugunarsu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG