WASHINGTON, D. C. - Kuri'ar da aka kada kan kudirin da jam'iyya mai mulki ta African National Congress ta goyi bayansa, na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya gana da wasu shugabannin kasashen duniya, inda ya zargi Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Gaza tare da kai farmakin soji a yankin da aka yi wa kawanya domin neman jagororin mayakan Hamas.
Kudirin da jam'iyyar adawa ta Economic Freedom Fighters ta gabatar ya samu goyon bayan 'yan majalisar 248 yayin da 'yan majalisa 91 suka nuna adawa da shi.
Kuri'ar ta zo ne bayan da ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce ta kira jakadanta a Afirka ta Kudu, Eliav Belotserkovsky, ya koma Kudus wato Jerusalem "don tattaunawa."
Dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu ta yi tsami sakamakon yakin Gaza. A baya Ramaphosa ya ce kasarsa ta yi amanna cewa Isra'ila na aikata laifukan yaki a Gaza, inda aka kashe dubban Falasdinawa.
-AP
Dandalin Mu Tattauna