Lamarin da ke kara dagula al'amura a tsakanin al'ummomin bayan da Afirka ta Kudu ta zargi Isra'ila da aikata kisan kare dangi a babban kotun Majalisar Dinkin Duniya.
Ministar harkokin wajen kasar Naledi Paindor ce ta bayyana hakan a farkon wannan mako a wani taron nuna goyon bayan Falasdinu da ya samu halartar jami'an jam'iyyar ANC ko African National Congress mai mulkin kasar Afirka ta Kudu.
Ta kuma karfafa gwiwar mutane da su yi zanga-zanga tare da rike tutoci dauke da kalaman "A dakatar da kisan kiyashi" a wajen ofisoshin jakadanci na abin da ta kira "magoya bayan Isra'ila biyar" a Gaza. Ba ta bayyana magoyan ba amma kusan tana nufin Amurka, Burtanniya da Jamus da sauransu.
"Na riga na fitar da wata sanarwa da ke fadakar da ‘yan Afirka ta Kudu da ke yaki tare da Sojojin Isra'ila: A shirye muke a lokacin da za ku dawo gida, mu kama ku,” in ji Pandor.
A watan Disamba, ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce gwamnatin Afirka ta Kudu ta damu da cewa wasu daga cikin 'yan kasarta ko mazaunan din-din-din sun shiga cikin rundunar sojin yakin Isra’ila (IDF) don yin yaki a Gaza, ta kuma yi gargadin cewa za su iya fuskantar shari'a idan ba a ba su izinin yin hakan ba.
Ba a dai bayyana ko ‘yan kasar Afirka ta Kudu nawa ne suke yaƙi da Isra’ila a Gaza ba.
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta kasance mai goyon bayan al'ummar Falasdinu kuma mai sukar Isra'ila tun kafin ma yakin na yanzu.
Batun dai na da tasiri a jam'iyyar ANC mai mulki da kuma 'yan kasar Afirka ta Kudu da dama, wadanda shekaru da dama suna kwatanta manufofin Isra'ila kan Falasdinawa a Gaza da Yammacin Kogin Jordan da mu'amalar wadanda ba fararen fata ba a Afirka ta Kudu a zamanin mulkin wariyar launin fata na nuna wariya da zalunci.
Isra'ila ta musanta zargin da Afirka ta Kudu ta yi na cewa tana nuna wariya a kan Falasdinawa a Yammacin Kogin Jordan da Gaza, kuma ta yi watsi da kakkausar murya kan tuhumar da Afirka ta Kudu ta yi a kotun duniya na cewa tana aikata kisan kiyashi a Gaza. Wannan shari'ar na iya ɗaukar shekaru kafin a yanke hukunci.
Isra'ila ta kuma mayar da martani inda ta zargi Afirka ta Kudu da kasancewa wakiliyar kungiyar Hamas da ta kai hari a kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, inda ta kashe 'yan Isra'ila kusan 1,200 tare da garkuwa da mutane 250 da aka yi garkuwa da su zuwa Gaza, lamarin da ya janyo yakin.
Hare-haren da Isra'ila ta kai kan Gaza ya kashe Falasdinawa sama da 31,000, ya kuma kori mafi yawan mutanen yankin gabar tekun miliyan 2.3 daga gidajensu tare da haifar da bala'in jin kai, yayin da dubban daruruwan Falasdinawa ke cikin matsanacin yunwa.
~ AP
Dandalin Mu Tattauna