Shugaban Kenya Ya Rusa Majalisar Ministocinsa Bayan Shafe Makonni 2 Ana Zanga-Zanga

Shugaban kasar Kenya William Ruto a Nairobi

A yau Alhamis Shugaba William Ruto na kasar Kenya ya sallami kusan dukkanin ministocinsa sannan ya sha alwashin kafa sabuwar gwamnati da za ta kunshi mambobi kalilan tare da aiki yadda ya dace sakamakon makonni da aka shafe ana zanga-zangar adawa da karin haraji da rashin iya mulki.

A jawabin da ya gabatar ta kafar talabijin, shugaban kasar ya sallami antoni janar din kasar sannan yace manyan sakatarori ne zasu cigaba da gudanar da ma’aikatun kasar.

Shugaba Ruto yace ya yanke hukuncin ne bayan daya saurari al’umma sannan zai kafa faffadar gwamnati bayan kammala tuntuba.

Kenya ta shafe makonni 3 tana fuskantar hatsaniya inda masu zanga-zanga suka afkawa ginin majalisar dokokin kasar a ranar 25 ga watan yunin daya gabata bayan da aka zartar da wani kudiri akan shirin kara haraji.

Zanga-zangar tayi sanadiyar mutuwar fiye da mutane 30, abinda ya rikide zuwa kiraye-kirayen neman shugaban kasar yayi murabus.

Yace Babban Sakataren Majalisar Ministocin, Musiala Mudavadi, babban abokinsa na siyasa zai cigaba da zama akan mukaminsa.

-AP