Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Sudan Ta Kudu Da Kungiyoyin 'Yan Tawaye Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Kenya


Kenya da Sudan Ta Kudu Sun Rattaba Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin ‘Yan Tawaye
Kenya da Sudan Ta Kudu Sun Rattaba Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin ‘Yan Tawaye

A ranar Alhamis gwamnatin Sudan ta Kudu da kungiyoyin 'yan tawaye suka rattaba hannu kan "yarjejeniya" samar da zaman lafiya a yayin tattaunawar neman sulhu a kasar Kenya, wanda aka bayyana a matsayin muhimmin mataki na kokarin kawo karshen rikicin Sudan ta Kudu da ya durkusar da tattalin arzikinta.

WASHINGTON, D. C. - Ba a bayyana abin da yarjejeniyar ta kunsa ba yayin bikin rattaba hannun, wanda ya samu halartar jami'an diflomasiyya da kungiyoyin farar hula.

Kenya - Sudan Ta Kudu
Kenya - Sudan Ta Kudu

Kungiyoyin 'yan adawar dai ba sa cikin yarjejeniyar shekara ta 2018 da ta kawo karshen yakin basasar Sudan ta Kudu da ya yi sanadin mutuwar mutum 400,000 tare da raba miliyoyi da matsuguninsu.

Ofishin harkokin wajen Kenya ya ce yarjejeniyar ta kasance wani mataki na farko a tattaunawar da ake ci gaba da yi inda bangarorin da ke gaba da juna suka yi alkawarin kawo karshen rikicin da tashin hankali.

Kenya - Sudan Ta Kudu
Kenya - Sudan Ta Kudu

A farkon tattaunawar shiga tsakani da aka kaddamar mako guda da ya gabata, shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya godewa takwaransa na Kenya, William Ruto, kan karbar bakuncin tattaunawar.

An yi wa tattaunawar lakabin Tumaini, Swahili don bege, hikima, kuma tsohon kwamandan sojojin Kenya Lazarus Sumbeiywo ne ke jagorantar tattaunawar.

Kenya - Sudan Ta Kudu
Kenya - Sudan Ta Kudu

A watan Disamba ne Sudan ta Kudu za ta gudanar da zabuka, amma har yanzu tana fama da tabarbarewar siyasa, a wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018 da ba a kammala aiwatar da ita ba, kuma saboda ana ci gaba da rikici da tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na kasar saboda bambancin kabilanci da siyasa.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG