Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Ruto Ya Ce Zai Yi Aiki Da Matasan Kenya Bayan Matsin Lamba Da Ya Sha Daga Matasan


Majalisar wakilai William Ruto (file photo)
Majalisar wakilai William Ruto (file photo)

Wani jami’in fadar shugaban kasar Kenya ya fada yau Lahadi cewa shugaban kasar na Kenya William Ruto ya ce a shirye yake ya tattaunawa da dubban matasa da suke zanga zanga a fadin kasar a wannan mako domin nuna rashin amincewar su da kudurin karin haraji.

A karkashin jagorancin wata hadakar matasan Kenya ta 'Gen-Z' da ta rika yada zanga-zangar kai tsaye ta yanar gizo, ta ce zanga-zangar ta zo wa gwamnati ba-zata, wanda aka gudanar kan rashin gamsuwa da manufofin tattalin arziki na Ruto.

"Matasan mu sun tashi haikan wajen shiga harkokin kasar su. Sun yi aikin su na dimokuradiyya, don su tsaya kuma a san da su. Ina alfahari da su," in ji Ruto a cikin furucinsa da kakakin fadar shugaban kasar Hussein Mohamed ya raba kan dandalin X, wanda a baya aka sani da Twitter.

Ya kara da cewa, "Za mu tattauna da ku don gano al'amuranku da yin aiki tare a matsayin kasa," in ji shugaban, lokacin da ya yi tsokaci na farko a bainar jama'a kan zanga-zangar.

Mutane biyu sun mutu kana wasu da dama sun jikata a zanga zangar da aka gudanar a Nairobi babban birnin kasar, a cewar masu rajin kare hakkin bil Adama.

Galibi an yi zanga zangar cikin lumana, amma jami’ai sun harba hayaki mai sa hawaye da kuma ruwan zafi yayin gudanar da tattakin a wani yunkurin hana masu zanga zangar isa ga majalisar dokoki.

An fara gudanar da tarukan gangami a ranar Talata kafin ya bazu zuwa ko ina a fadin kasar, inda masu zanga zangar ke kira ga yin yajin aiki na kasa baki daya a ranar 25 ga watan Yuni.

Gwamnatin Ruto ta kare kudurinta na fito da sabbin haraji da kasar ke bukata domin dogaro da kai da kuma rage yawan dogaro da karbar rance daga kasashen waje.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG