Wani sabon zagayen zanga zanga ya sake barkewa a Nairobi, babban birnin Kenya da sauran sassan kasar a jiya Talata, biyo bayan mummunar zanga zangar makon jiya kan sabuwar dokar kudi ta Shugaban kasar William Ruto da ya hada da karin haraji, domin biyan dimbin bashin da ake bin kasar.
Yan sanda sun rika harba hayaki mai sa hawaye akan masu zangazangar a birnin Nairobi, inda cibiyoyin kasuwanci suka kasance a rufe saboda tsoron wawaso.
An rufe babbar hanyar zuwa Mombasa, birni na biyu mafi girma a kasar, sakamakon kona tayoyi da masu zanga zangar suka yi akan hanyar.
Shugaba Ruto dai na fuskantar rikici mafi muni tun bayan da ya kama aiki a shekarar 2022, inda wasu masu zanga zangar ke kiran ya sauka daga shugabancin kasan, suna mai zargin shi da rashin iya mulki.
A cikin makon jiya, ne Majalisar dokokin kasar ta amince da kudurin dokar kudin, tsaka da zanga zangar wadda ta rikide ta yi munin gaske lokacin da masu zanga zangar su ka kutsa cikin ginin Majalisar a birnin Nairobi, inda yan sanda su ka bude wuta, su ka kashe mutane sama da 20 a cewar, kungiyoyin kare hakkin bil’adama.
A farkon ballewar rikicin, shugaba Ruto yace, ba zai sanya hannu akan kudurin dokar ba, ya kuma yi kiran da a gudanar da bincike kan mace- macen masu zanga zangar. To sai dai bisa ga dukkan alamu, hanzarin na Ruto bai samu karbuwa ba a gurin matasan 'yan fafutuka, wadanda ke neman Shugaban kasar ya san inda dare yayi mishi ya sauka daga shugabancin kasar.
Dandalin Mu Tattauna