Rundunar ‘yan sandan ta kuma rufe majalisar, inda ‘yan majalisar ke tafka mahawara kan kudirin kara harajin, da kuma fadar shugaban kasa, wurin ofishin shugaban kasa da gidan sa yake.
Masu shirya zanga-zangar dai sun yi kira da a gudanar da zanga-zanga da kuma yajin aikin gama-gari na adawa da dokar harajin da fatan za a ci gaba na tsawon mako guda, lamarin da ya mayar da yunkurin da matasa ke yi a yanar gizo ya zama babban ciwon kai ga gwamnati.
Masu zanga-zangar sun kuma yi kira ga shugaba William Ruto da ya sauka daga karagar mulki.
Ruto ya lashe zaben da aka gudanar ne kusan shekaru biyu da suka gabata a kan wani tsarin da zai jagoranci talakawan Kenya masu aiki, amma ya tsinci kan shi tsakanin bukatun masu ba da lamuni kamar asusun lamuni na duniya IMF, wanda ke kira ga gwamnati da ta rage gibi, da kuma al'ummar da ke fama da tsadar rayuwa a kasar.
'Yan jaridar Reuters sun ce yayin da masu zanga-zangar suka gudanar da zanga-zanga a ranar Talata, 'yan sanda sun harba barkonon tsohuwa a yankin tsakiyar kasuwanci da kuma garin Kibera.
Daruruwan mutane kuma sun yi tattaki a kan titunan birnin Mombasa da ke gabar teku, a Kisumu, wani tashar jiragen ruwa a tafkin Victoria, da kuma sauran garuruwa, kamar yadda gidan talabijin na Kenya ya nuna.
'Yan sanda dai sun tarwatsa duk wadanda suka taru a titunan da ke kewayen majalisar kasar a birnin Nairobi.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna