Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Afirka

Masu Fafutuka A Kenya Sun Yi Kira Da A Fita Zanga-zanga Ranar Talata


Nairobi, June 27, 2024.
Nairobi, June 27, 2024.

Masu fafutuka a kasar Kenya sun yi kira ga masu zanga-zanga da su sake fitowa kan tituna a ranar Talata, inda da yawa suka yi watsi da rokon da shugaban kasar William Ruto ya yi na a tattauna bayan matakin da ya dauka na janye shirin kara haraji.

Nairobi, (File photo).
Nairobi, (File photo).

Akalla mutum 24 ne suka mutu sakamakon arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zangar da 'yan sanda a makon da ya gabata, lokacin da aka kai wa majalisar dokokin kasar hari na kankanin lokaci tare da cinna wuta.

Zanga-zangar wacce matasa ne suka jagoranta kuma aka shirya ta a shafukan sada zumunta, tun da farko ta taso ne sakamakon wani kudirin doka da aka yi niyyar tara harajin kudi shilling na Kenya biliyan 346 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2.69.

KENYA
KENYA

Sai dai bukatun masu zanga-zangar da dama sun kara ta'azzara cikin makonni biyun da suka gabata da hadawa da kiraye-kirayen kawar da cin hanci da rashawa da kuma neman shugaba Ruto ya sauka daga karagar mulki, lamarin da ke nuni da rikicin da ya fi kamari a mulkinsa na tsawon shekaru biyu.

Da alama wata hira da Ruto ya yi a yammacin Lahadin da ta gabata da gidajen talbijin na Kenya, inda galibi ya ke kare matakin ‘yan sanda da gwamnatinsa, ta kara ingiza matsayin masu zanga-zangar ne.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG