Sakamakon zaben Misra

Garin Fayoum, gari ne dake kudancin birnin Alkahira wanda yayi kaurin suna da masu tsatsauran ra'ayin Islama, amma ga dukkan alamu, yanzu hakkar mazauna garin na dab da cimma ruwa wajen samun hanyar warware matsalolin siyasar kasar baki daya.

A karo na biyu hukumar zaben kasar Masar ta jinkirta bayyana sakamakon zaben da aka gudanar na ‘yan majalisar dokoki.

Anji wani jami’in hukumar zaben Misra a yau Alhamis yana cewa sakamakon zaben da tun farko aka shirya bayyanawa ran Alhamis an sake dagawa har zuwa gobe Juma’a.

Babban jami’in hukumar zaben ta Misra yana mai cewa babban dalilin jinkirin shine ganin yadda har yanzu ba’a kammala kidaya kuri’un zagayen farko na zaben ‘yan majalisar wakilai ba.

Tun farko an shirya bayyana sakamakon zaben da aka gudanar a mazabun birnin Alkahira, da Alxandria da wasu mazabu bakwai ran laraba, amma sai hakan bai samu ba. Wannan zabe shine irinsa na farko a Misra tun hambaras da shugaba Hosni Mubarak a watan Fabarairun da ya gabata. Ga dukkan alamu, hadin gwiwar kungiyar Muslim Brotherhood da sauran jam’iyyun ra’ayin rikau karkashin Inuwar jam’iyyar al-Nour Salafi ne zasu sami gagarumar nasara a zaben Majalisar dokokin na kasar Misra.

Aika Sharhinka