Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kasa Da Kasa Tana Tuhumar MInistan Tsaron Sudan

Shugaba Omar Hassan al-Bashir na Sudan (file photo).
Shugaba Omar Hassan al-Bashir na Sudan (file photo).

Babban mai gabatar da kara gaban kotun kasa da kasa Luis Moreno Ocampo, ya bukaci kotun ta bada sommacin a kama ministan tsaron Sudan, Abdulrahim Mohammed Hussein, kan zargi aikata laifuffukan yaki a yankin Darfur.

A cikin sanarwa da ya bayar yau jumma’a Mr. Ocampo yace ministan tsaron zamanin yana ministan cikin gidan Sudan, tsakanin 2003-2004 yana da hanu wajen kitsa kai hare hare kan kauyuka a yankin na Darfur da ake yi kawanya, san nan jiragen yakin kasar su kai musu harin bam, daga bisani sojoji da mayakan sakai da ake kira “janjaweed’ su kashesu da fyade.

Tilas alkalan kotun su yi nazarin shaidar da aka bayar san nan su yanke hukunci ko zasu amince da bada sommaci aka ministan.

Ahalin yanzu kuma shugaba Omar al-Bashir na Sudan ya gana da ministan harkokin wajen Kenya jiya Alhamis a Khartoum a kokarin warware rikici tsakanin kasashen biyu, wadda ya biyo bayan hukuncin da wani alkali a Kenya ya yanke na neman a kama shugaba al-Bashir, kamar yadda kotun kasa da kasa ta nema, idan ya sake taka kafarsa ya shiga Kenya.

Aika Sharhinka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG