Dubun dubatan ‘yan Misra sun taru a dandalin Tahrir na birnin al-Khahira a jiya Jumma’a inda su ka yi ta jaddada bukatarsu ta neman a kawo karshen mulkin soji duk ko da nada sabon Firayim Minista da gwamnatin mulkin sojin ta yi.
Yawan masu zanga-zangar ya yi ta karuwa a tsawon sati gudan da ya gabata, duk ko da jerin sauye-sauyen da gwamnatin ta sanar. A kalla mutane 41 ne aka kashe a tashe-tashen hankulan da ke da nasaba da zanga-zangar a fadin kasar.
Ana cigaba da tashe-tashen hankulan ne a sa’ilinda Misra ke shirye-shiryen fara zaben Majalisa a ranar Litini. Zaben zai kasance na farko tun bayan murabus din da tsohon shugaba Hosni Mubarak ya yi cikin watan Fabrairu sanadiyyar wata gagarumar zanga-zanga.