'Yan kasar Masar sunyi caa a rumfunan zabe a yau Laraba a zagaye na biyu na zaben wakilan Majalisar wakilan kasar, a yayinda jam'iyun Islama suke fatar kara yawan wakilansu.
A yankunan guda tara ake zaben na yau Laraba, ciki harda Aswan da Beni Suef da Giza da Ismaila da Suez da kuma Sohag. Fiye da yan kasar miliyan goma sha takwas ne suka cancanci jefa kuri'a a zagaye na biyu na zaben da za'a kamalla Alhamis din nan
Masu zabe, suna zaben wakilan Majalisar wakilai dari hudu da casa'in da takwas. Jam'iyar Muslim Brotherhood's Freedom da kuma jam'iyar Al Nour Salafi mai ra'ayin rikau sune suka kanainaiye zagaye na farko na zaben da aka yi.
Wasu kasashen yammacin duniya suna fargabar nasara da jam'iyun Islama suke samu. Suma wasu Musulmi suna nuna damuwa, suna kashedi akan irin yancin da ake dasu a kasashen yammacin duniya kamar baiwa yan luwadi yancin yin aure a tsakaninsu da dai sauransu. Suna yin wannan gargadi ne domin samun goyon bayan mutane a yankunan karkara.
A farkon watan Janairu idan Allah ya kaimu za'a yi zagaye na uku a zabe a lardunan da suka rage