Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A yau litinin Misrawa ke zaben ‘yan majalisar dokoki


Matar Misra cikin Hijabi ke kokarin jefa kuri'a a birnin Alkahira a zaben ranar litinin.
Matar Misra cikin Hijabi ke kokarin jefa kuri'a a birnin Alkahira a zaben ranar litinin.

A karon farko tun hambaras da shugaba Hosni Mubarak na Misra a watan Fabarairun da ya gabata,anga dogayen layukan masu son kada kuri’a kusan a kowace mazaba a kasar Misra, mutane na dokin samun sukunin jefa kuri’arsu a tsarin salon mulkin Dimokuradiyya.

A tattaunawar da wakilin Muryar Amurka, masu jefa kuri’a sun yi fatan za’a basu wadanda suka zaba ba kamar sauran zabukan baya ba da suka ce an tafka magudi. Dalibar Jami’a, Farah a cikin lullibinta na Hijabi tana kan layin mata dake son jefa tasu kuri’a tace wannan zaben na yau, wani zakaran gwajin dafin makomar siyasar kasar Misra ne domin an baiwa matan Misra damar sanya hannu a duk ala’muran ci gaban kasar su Misra. Tace taso kada kuri’ar a zaben shekarar da ta gabata, amma mushkilar itace babu tabbas ko yin zaben zai tabbatar da bata damar ci gajiyar ‘yancinta da damar tsoma baki a harkokin siyasar kasar Misra. Amma a yau, tace ga dukkan alamu za’a bata wannan dama. Shi yasa aka ganta a layin masu kada kuri’a. A rumfunan zaben birnin Alexandria inda ake shirin gudanar da zabe har zagaye biyu, anji wani da yace shike Magana da yawun kungiyar Moslem Brothers yana cewa an dan sami tangarda wajen tura akwatunan zabe tun da farko, ba’a kaisu a kan lokaci ba sai can tsakar dare.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG