Misrawa suna ci gaba da tururuwa zuwa dandalin Tahrir dake Alkahira, suna kira da a kawo karshen mulkin soja.
Dubun dubatan Misrawa ne cikin fushi suka cika dandalain da yanzu yayi kaurin suna. Tun da safiyar yau har zuwa lokacin sallar jumma’a suka shiga sahun kuwwar “Yanci, ‘Yanci”.
Wasu masu zanga zanga suna buga kirjin “ganagamin mutum milyan daya, ya kasance dama ta karshe ga sojoji dake mulkin kasar suyi abinda yafi dacewa su yi murabus. Amma maimakon mika mulki ga gwamnatin farar huka majalisar mulkin sojinn kasar ta nasda sabon PM, mutuminda ta nada shine Kamal Ganzouri.
Tunda farko wata jaridar kasar Al Ahram ta ce Ganzouri ya amince zai jagoranci gwamnatin ‘Yanta kasa:, bayan ya gana da shugaban majalisar mulkin sojin kasar Field Marshall Husein Tantawi. Mr. Ganzouri ya tab rike wan nan mukami a zamanin mulkin Hosni Mubarak.
Wan nan mataki ko kusa bai yi tasiri kan masu zanga zanga ba.
Kamfanin dillancin labaran faransa ya bada labarin cewa limamin da ya jagoranci sallar jumma a a dandalinn Tahrir yay i kira masu zanga zanga da kada su waste daga dandalin har sai sun sami biyan bukata. Wasu daga cikin masu zanga zangar sun ce basu da niyyar warsewa har sai sunga abinda ya turewa buzu nadi.