Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush Ya Ce Dole A Ci Gaba Da Yaki Da Cutar AIDS


Tsohon shugaban kasar Amurka George W. Bush ya na tsaye a kusa da wata mata mai dauke da kwayar HIV mai haddasa cutar AIDS ko SIDA a asibitin kwalejin koyarwa na Saint Paul Millenium a birnin Addis Ababa, kasar Ethiopia
Tsohon shugaban kasar Amurka George W. Bush ya na tsaye a kusa da wata mata mai dauke da kwayar HIV mai haddasa cutar AIDS ko SIDA a asibitin kwalejin koyarwa na Saint Paul Millenium a birnin Addis Ababa, kasar Ethiopia

Mr. Bush ya ce Amurkawa su sani, karimci da halin su na kyauta sun ceci rayukan jama'a da dama

Tsohon shugaban kasar Amurka, George W.Bush, ya ce duk da fargabar da matsalar tattalin arzikin duniya ta haifar, lallai dole ne a ci gaba da yaki da cutar AIDS, ko SIDA ; ya fadi hakan ne a wajen babban taron da ake yi a kan cutar ta AIDS.

A jawabin bude taron da yayi a jiya Lahadi a Addis Ababa, babban birnin kasar Ethiopia, Mr.Bush yace tabbas ne kasashen duniya su tsara abubuwan baiwa fifiko, "amma babu abun da ke da fifiko fiye da ceton ran Dan Adam".

Haka kuma ya karfafawa gwamnatin Amurka guiwar kasancewa bisa kudirin ceton rayukan 'Yan Adam a kasashe masu tasowa da kuma bayar da kudaden gudanar da ayyukan yaki da cututtukan da ke yaduwa ta hanyar jima'i, ya ce ko da yaushe ita manufar siyasar ware kai a ki yin huldar taimakawa wasu kasashe, manufa ce ta karancin dogon tunani da rashin hangen nesa.

Mr.Bush wanda ke tare da uwargidan shi da 'ya'yan su mata biyu, ya kammala rangadin da yake yi a Afirka wanda ya fara da kasashen Tanzania da Zambia.

An karrama tsohon shugaban kasar na Amurka ne saboda rawar da ya taka wajen kirkiro da shirin PEPFAR, wato shirin shugaban kasa na gaggauta yaki da cutar AIDS. Daga lokacin da aka kafa shirin a shekarar dubu biyu da uku, wanda aka bayyana cewa shi ne shirin kula da lafiya mafi girma a fannin yaki da cutar AIDS, ya baiwa kasar Ethiopia dola miliyan dubu daya da miliyan dari hudu.

Shirin PEPFAR ya taimaka da jimlar kudi kimanin dola miliyan dubu talatin da tara ga shirye-shiryen kasa da kasa na yaki da cutar HIV/AIDS da, masassarar cizon sauro da kuma ciwon tarin fuka wato TB.

Mr.Bush ya shaidawa wakilin gidan Rediyon Muryar Amurka a birnin Addis Ababa cewa Amurkawa na bukatar sanin cewa karimcin su da kuma halin su na kyauta sun ceci rayukan jama'a masu dimbin yawa.

Aika Sharhinka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG