Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Misra ta ce an fito kada kuri'a sosai


Layin masu kada kuri'a a zaben Misra
Layin masu kada kuri'a a zaben Misra

Jami’an hukumar zaben Misra sun ce an fito da dama don kada kuri’a

Jami’an hukumar zaben Misra sun ce an fito da dama don kada kuri’a wannan satin, a karo na farko na zaben Majalisar Dokokin kasar tun bayan juyin-juya hali.

Kwamishinan zaben, Abdel-Mooaez Ibrahim, ya fadi jiya Jumma’a cewa yawan fitowa zaben a ranakun Litini da Talata a daya bisa ukun lardunan kasar ya kai kashi 62%. Ya ce ‘yan Misra fiye da miliyan 8 ne su ka kada kuri’a.

Kodayake Shugaban hukumar zaben ya bayar da wasu sakamakon zaben Majalisar Wakilai, bai bayyana abin da kowace jam’iyya ta samu ba. Ya ce ya gaji- don haka ya ce da ‘yan jarida su dubi sakamakon zaben da kansu. Sannan sai kwatsam ya katse taron manema labaran.

Tun da farko, masu nazarin al’amuran yau da kullum sun yi hasashen cewa jam’iyyar ‘yan Muslim Brotherhood mai suna Freedom and Justice Party, (ko Jam’iyyar ‘yanci da adalci) da kuma wata wadda ta fi ra’ayin rikau, mai suna al-Nour Salafi ta masu kishin Islama, su ne za su yi rinjaye.

Sau biyu jami’an zaben ke jinkirta sanarwar sakamakon zaben, su ka ce su na bukatar karin lokaci don kidaya kuri’un.

Masu kada kuri’a a sauran lardunan za su kada kuri’ar ce a matakai biyu a ‘yan makwanni masu zuwa. Sannan kuma ‘yan kasa gaba daya su yi zaben Majalisar Dattawa. Sai cikin watan Maris mai zuwa a kallama komai.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG