Rahotanni daga Rasha sun ce ana shirin afkawa birnin Alepo dake Syria

Syria

Rahotanni daga kasar Rasha na cewa ana wani gagarumin shirin afkawa birnin Aleppo saboda kwatoshi daga hannun 'yan tawaye da suka kawashe fiye da shekaru biyu suna rike da birnin.

Labarai daga Rasha na fitowa game da cewa Sojojin Syria na shirin kai wani gagarimin harin da ke da nasaba da tsaro, tare da hadin gwiwar sojojin yakin saman Rasha don sake kwato ikon birnin Aleppo da ake ta faman artabu.

A jiya Lahadi kamfanin dillancin labaran Interfax ya kalato inda Firayim Ministan Syria Wael Alhaiqi na cewa, wannan kutsawar sojan na nufin kakkabe duk wani tarnakin masu dauke da makamai ba bisa doka ba.

Wadanda kuma su basu tsayawa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka yi a watan Fabrairun da ya gabata ba, ba su kuma karya yarjejeniyar ba. Haiqi ya kara da cewa, sake kwace garin zai sharewa sojoji hanya ta kusan kilomita 300 daga gabashi.

Wan nan ne hanyar da zata kai dakarun har Deir Ezzor da ke daya daga wuraren da ‘yan tawayen ke da karfi matuka kuma suke rike da ikon wajen. Aleppo dai a baya itace cibiyar tattalin arzikin Syria.