Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD: Wakili Steffan Mistura zai gana da 'yan adawar Syria


Wakilin MDD Staffan de Mistura
Wakilin MDD Staffan de Mistura

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice kan batun kasar Syria, Staffan de Mistura, yana sake ganawa yau Litinin da wakilan ‘yan adawar kasar a birnin Geneva.

Ganawar ta biyo bayan da aka samu ci gaba a kokrin warware wasu daga cikin batutuwan da babbar kungiyar masu adawa ta nemi a takala kafin a fara tattaunawar yin sulhu.

De Mistura ya jinkirta ganawar da ya shirya yi da jami’an gwamnati a yau litinin domin ya samu sukunin ganawa da ‘yan adawar kafin nan.

Ya fada jiya lahadi cewa yana da kwarin guiwa kuma ya kudurci aniyar gajnin ‘yan adawa sun shiga cikin tattaunawar ta neman sulhu da aka fara ranar jumma’a, inda su wakilan adawar suka kauracewa ranar farko.

Wani kakakin ‘yan adawar na Syria yace sun samu kwarin guiwa, kuma tattaunawa ta yi alfanu jiya lahadi kan batun ayyukan jinkai. Yana magana ne kan bukatar da kungiyar ta gabatar cewa a kawo karshen hare-hare ta sama kan yankunan fararen hula, a kuma kawar da killacewar dake hana kayan agaji isa ga yankunan dake hannun ‘yan tawaye.

XS
SM
MD
LG