A cikin sanarwan bazata da Kungiyar tarayyar turai ta bayar tace ba zata bada kai bori ya hau ba domin ganin an mayar da ‘yan gudun hijira daga tsibirin Girka zuwa kasar Turkiyya ba, a kokarin da ‘yan kungiyar kare hakin bil adama keyi. Na ganin anyi hakan.
Mai Magana da yawun kungiyar Jean-Pierre Schembri ya shaidawa wani wakilin wannan gidan Radiyon VOA,cewa kungiyar ta yanke hukuncin baiwa dukkan wani dan gudun hijira damar ya nemi iznin mafaka kafin a aika dashi Turkiyya kamnar yadda sharauddan da aka shinfida ya tanada kuma ya fara aiki a ranar littinin data gabata.
Yanzu haka dai dai ‘yan gudun hijira da yawan su yakai 200 ne suka isa bakintsibirin Girka, kuma aka kaisu Turkiyya a ranar littini domi musayar su da ‘yan kasar Syria wadanda alka samar wa mafaka a sansanin dake kasar ta Turkiyya.
Haka kuma a ranar juma ne ake sa ran wasu ‘yan gudun hijirar har su 200 da za a yi musayar su ranar jumaa, sai dai kungiyyar Tarayyar ta Turai tace za a baiwa ko wane dan gudun hijira damar kwanaki biyar domin neman mafaka kafin ace a mayar dashi.