Haka kuma suna mika bukatar bangarorin gwamnati da na ‘yan tawaye da su saki fursunonin juna da suka kama.
Musamman ma wadanda basu jib a basu gani ba a rikicin. Bayan taron sa’o’i 4 a birnin Moscow, Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da Shugaban Rasha Vladimir Putin, sun amince da cewa, hadin kai tasakani manyan kasashensu guda 2 zai taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen yakin Syria.
Kerry yace yana sane da karya ka’idojin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka tsara, amma yace suna nan suna yiwa abin kallon kurilla. Kerry da takwaransa na Rasha Sergie Levrov sun yi taron manema labarai na hadin gwiwa a yammacin jiya a birnin Kremlin bayan doguwar tattaunawar da aka yi.
Ministan wajen Amurkan yayi kira ga Rasha da ta saki direbar jirgin saman yakin nan ‘yar kasar Ukraine Nadiya Savchenco da suka yankewa hukuncin shekaru 22 a gidan yari. Sai dai Levrov bai dauki wani alkawarin yin hakan ko kuma a’a ba.