Jan Egeland, shugaban kwamitin Majalisar Dinkin Duniya a taron da ake yi kan batutuwan jinkai a Jamus, inda aka cimma wannan yarjejeniyar, yace “sai tayiwu wannan ne budin da ake dako.”
Miniustan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya fada ta shafinsa a dandalin Twitter yau Jumma’a cewa, “wannan mataki yana da muhimmanci kan hanyar samo damar warware rikicin da ake yi a Syria.”
Sai dai anji Firayim Ministan Syria Dmitri Medvedev, yana gargadin manyan kasashen duniya cewa suyi tunani gameda tura sojojin-kasa zuwa Syria. A cikin sanarwa da ya bayar yau Jumma’a, yace, matakin sojin kasa zai iya tsunduma dukkan kasashe dake aiki kan rikicin cikin yaki.
Kerry ya gayawa manema labarai a birnin Munch cewa, shirin tsagaita wutar ba zai shafi kungiyoyin ‘yan ta’adda ba, da suka hada da ISIS, Al-Nusra d a dai sauransu.