Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Rasha Zata Fara Janye Sojojinta Daga Syria


Shugaban kasar Rasha
Shugaban kasar Rasha

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya bada umarnin janye dakarun kasar daga Syria, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke jagorantar wani sabon zaman tattaunawar wanzar da zaman lafiya kan Syria a Geneva.

Tashar watsa labarai ta kasar Rasha ta ambaci ta bakin shugaba Putin jiya Litinin, yana gayawa ministan tsaron kasar Sergei Shoigu da ministan harkokin kasashen ketare Sergei Lavrov cewa, an cika burin nauyin da aka dorawa ma’aikatar tsaro a Syria.

Putin ya shaidawa ministocin cewa. “saboda haka, nake bada umarnin daga gobe, a fara janye dakarunmu daga Syria dake jamhuriyar Larabawa.

Shafin sadarwar internet na Kremlin ya ambaci ta bakin Putin yana shaidawa shugaban kasar Syria Bashar al-Assad ta wayar tarho cewa, zai janye muhimmin rukunin mayakan saman Rasha dake aiki a Syria.

A Damascus, ofishin shugaban kasar Syria yace Assad ya yi na’am da wannan yunkurin, sai dai ya kara da cewa, Rasha tayi alkawarin cewa, mayakan samanta ba zasu janye daga Syria baki daya ba.

Fadar white ta bayyana cewa, shugaban Amurka Barack Obama ya kira Putin jiya Litinin domin tattauna batun janyewar, da kuma yadda za a ci gaba da tattaunawa da Syria game da harkokin siyasar kasar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG