Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Syria: Kayan abinci zasu fara isa garuruwan da mutane suka soma mutuwa saboda yunwa


Yankin Idlib dake fama da yunwa
Yankin Idlib dake fama da yunwa

A yau Litinin, kayayyakin tallafi da suka hada da na abinci da magunguna da kuma barguna, sun kusa isa garurruwa uku a kasar Syria, inda yakin basasar kasar ya jefa mutanen yankin cikin halin matsaninciyar yunwa.

Ana sa ran kayayyakin za su isa Madaya, wani gari da ke kusa da iyakar Lebanon da kuma Fuaa da Kafraya da ke Lardin Idlib a kusa da iyakar Turkiyya.

Wannan kai doki da ake shirin yi, na samun hadin gwiwar kungiyar ba da agajin gaggawa ta Red Cross da reshen ta na Syria da kuma Majalisar Dinkin Duniya, bayan da hukumomin Syrian suka amince a bar kayayyakin su wuce.

Rahotanni sun ce fararen hula a wadannan yankuna, sun shiga halin kakani-kayi, yayin da fadan da ake yi da ‘yan tawaye da dakarun shugaba Bashar Al Assada ya shiga kusan shekara ta biyar.

Baya ga haka, akwai sauran bangarorin da ke cikin wannan fada wadanda suke adawa da gwamnatin ta Syria.

‘Yan tawayen Syria dai suke rike da garin na Madaya, lamarin da ya sa dakarun kasar suka datse hanyar kaiwa ga garin, wanda ke dauke da mutanme dubu 42.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG