Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Syria: Hare-haren jiragen sama sun lalata asibitin agaji na kungiyar MSF


Wurin da aka jefa bamabamai
Wurin da aka jefa bamabamai

Hare-haren jiragen sama a yau litinin sun lalata wani asibitin da kungiyar agajin likitoci ta MSF ke tallafawa, suka kashe mutane akalla 7, a yankin arewa maso yammacin kasar Sham ko Syria.

Kungiyar agajin ta MSF ta ce rokoki 4 sun fada kan ginin dake garin Maaret al-Numan a lardin Idlib. Ma’aikata 8 sun bace ba a san inda suke ba.

Shugaban tawagar ayyukan kungiyar a Sham, Massimiliano Rebaudengo, y ace da alamun wannan hari ne da aka kai da gangan a kan cibiyar kiwon lafiya, kuma muna yin tur da shi da kakkausar harshe in ji shi. Yace lalata wannan asibitin ya bar mutane dubu 40 dake zaune cikin wannan gari inda ake gwabza fada ba su da wata cibiyar lafiya.

Kungiyar ta ce wannan asibiti mai gadaje 30 na kwantar da marasa lafiya, yana da ma’aikata 54, da dakunan tiyata biyu da sashen sha ka tafi, da kuma dakin bayar da jinyar gaggawa.

Kungiyar sanya idanu kan kare hakkin bil Adama a Syria dake da hedkwata a Britaniya, ta ce an yi Imani jiragen saman yaki na Rasha ne suka kai wannan harin, suka kashe mutane masu yawa tare da raunata wasu.

Haka kuma a yau litinin din, wani makami mai linzami ya fada kan wani asibitin yara a garin Azaz na arewacin kasar ya kashe mutane akalla 10.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG