Nijar Ta Baiwa Sojojin Mali Da Burkina Faso Damar Shiga Kasar Idan Aka Kai Mata Hari

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Jamhuriyar Nijar ta bai wa sojojin Mali da Burkina Faso izinin shiga cikin kasarta idan har aka kai hari, a wata sanarwar hadin gwiwa da kasashen suka fitar a ranar Alhamis ta nuna.

WASHINGTON, D.C. - Wannan wata alama ce da ke nuna gwamnatin mulkin sojan ta Nijar na shirin ci gaba da bijirewa matsin lambar da yankin ke fuskanta da kin sauka da maida mulki ga hambararren Shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Shugaban sojojin Mali Assimi Goita

Kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka na kokarin tattaunawa da Shugabannin da suka yi juyin mulki amma ta yi gargadin cewa a shirye take ta tura dakaru zuwa Nijar domin maido da tsarin mulkin kasar idan yunkurin diflomasiyya ya ci tura.

Duk wani abin da ke kara ta'azzara yana iya kara dagula al'amura a yankin da ake fama da tashe-tashen hankula kamar yadda makwabtan Nijar da ke karkashin jagorancin mulkin sojan Mali da Burkina Faso suka ce za su marawa Nijar baya a duk wani rikici da kungiyar ECOWAS.

Manyan Hafsoshin Kungiyar ECOWAS

A ranar Alhamis din da ta gabata, ministocin harkokin wajen kawayen kasashen uku sun ce sun gana a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar, inda suka tattauna kan inganta hadin gwiwa a fannin tsaro da sauran batutuwa.

Gwamnatin Sojin Kasar Burkino Faso

Sanarwar ta ce, ministocin sun yi marhabin da rattaba hannu a ranar Alhamis da shugaban mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya sanya hannu kan wasu umarni biyu na "ba wa dakarun tsaro da tsaro na Burkina Faso da Mali izinin shiga tsakani kan yankin Nijar idan an kai hari."

Ministocin Burkina Faso da Mali, sun sake nanata kin amincewa da shigan karfi da makamai a kan al'ummar Nijar wanda za a dauke shi a matsayin shelanta yaki.

-Reuters