AGADEZ, NIGER - Duk da rashin gamsuwa akan yanayin da kasar take ciki tun bayan hambarar da zababben Shugaba Mohamed Bazoum, tsofaffin ‘yan tawayen wadanda suka taba yin tawaye a Nijar a can baya sun ce ba sa goyan bayan sake komawa harkokin tawaye.
Wannan na zuwa ne bayan da wani tsohon jagoran ‘yan tawaye a Nijar ya kaddamar da wani yunkuri na fafatwa da sojojin da suka yi juyin mulki a ranar 26 ga watan Yulin wannan shekarar, lamarin da ya sa tsofaffin ‘yan tawayen fitar da sanarwar kin amincewa da yunkurin tsohon madugun ‘yan tawaye Mohamed Lawren wanda yake daya daga cikin wadanda suka yi tawaye shekarun baya.
Kafa kungiyar da tsohon madugun ‘yan tawayen ya yi da manufar tallafawa kokarin dawo da aiki da tsarin mulki a Nijar alama ce ta farko ta bullar gwagwarmayar nuna bijirewa a cikin gida ga juyin mulkin da sojoji suka yi.
Sai dai su tsofaffin ‘yan tawayen sun yi kira ga al’ummar Nijar da su zama tsintsiya madaurinki guda, a cewar Malam Bilal Shima wani tsohon dan tawaye na Arewacin kasar.
Tsofaffin ‘yan tawayen dai sun bayyana rashin gamsuwarsu kan matakin ECOWAS na sanyawa Nijar takunkumai.
Sai dai sun yi fatan Kungiyar ta ECOWAS ta bi hanyar diflomasiyya don samun maslaha tsakanin ta da Shugabannin mulkin sojojin, maimakon amfani da karfin soja.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna