Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Juyin Mulkin Nijar Za Su Mika Mulki Ga Farar Hula Nan Da Shekara 3


Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Shugaban majalissar sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya bayyana fatan gudanar da al’amuran mulkin rikon kwaryar na tsawon wa’adin da bai kamata ya wuce shekaru uku ba.

NIAMEY, NIGER - Janar Tchiani da ke wannan bayani ta kafar talbijan a wani lokacin da tawwagar ECOWAS ta kai ziyara a Nijar don duba hanyoyin sulhu, ya soki lamirin kungiyar da wata babbar kasar da bai ambaci sunanta ba kan matakin amfani da karfin soja don mayar da zababben hambararren Shugaba Mohamed Bazoum akan mukaminsa muddin hanyoyin sulhu suka ci tura.

Janar Tchiani wanda ya fara jawabinsa da caccakar CEDEAO sakamakon jerin takunkumin da ta kakaba wa Nijer sanadiyar juyin mulkin da ya jagoranta, ya kuma zargi kungiyar da yunkurin kafa rundunar dakarun tsaro da nufin mamayar kasar. Ya na mai cewa bai kwaci mulki don ya dauwama a kan sa ba, saboda haka a shirye ya ke kan maganar sulhu tare da la’akari da abubuwan da ‘yan Nijar ke bukata.

Ya sake nanata cewa al’ummar Nijar da su ‘yan majalisar soja ta CNSP ba sa son yaki kuma a shirye su ke a shiga tattaunawa, to amma fa a gane cewa da zaran aka kaddamar da yaki akan wannan kasa to kada a yi zaton abin zai zo da sauki kamar yadda wasu ke tunanin haka domin zasu tarar da ‘yan Nijar million 26 jikokin sarakunan dauri.

Haka kuma a cewarsa askarawan Nijar da hadin guiwar takwarorinsu na Mali, Burkina Faso da Guinea ba za su yi kasa a gwiwa ba.

Kan batun mayar da mulki a hannun fararen hula, shugaban majalisar sojojin CNSP ya ce zai umurci gwamnatin rikon kwarya ta shirya taron tattauna sabuwar tafiyar da kasa za ta sa gaba.

Ya ce kungiyoyin rukunonin al’umma za su yi nazari a tsawon kwanaki 30 domin gabatar da shawarwarin da za su ba da damar tsara mahimman ka’idodin tafiyar da mulkin rikon kwarya, sannan su zakulo abubuwan da ya kamata a fi bai wa fifiko a tsawon wa’adin gwamnatin rikon kwaryar da bai kamata ya wuce shekaru uku ba, da dai sauran wasu muhimman matakan samar da sauyi a kasa.

Yanzu dai a fili take bangarorin da ke takaddama a rikicin siyasar da ya sarke a Nijar bayan juyin mulkin 26 ga watan Yuli sun ja daga, ko da yake a kowane bangare a na maganar sulhu, a dai gefe shirin kafsa yaki ya kankama.

Yayin da shugabanin rundunonin mayakan kasashen CEDEAO suka sanar da kammala tsare-tsare a karshen taronsu na Accra, a Nijar kuma tashar talbijan ta RTN mallakar gwamnati ta nuna wasu jiragen saman soji biyu da aka ayyana a matsayin dauki daga sojan Burkina Faso da Mali ga abokansu na Nijar.

Wani labarin da ke da alaka da wannan dambarwa kuma, sojojin juyin mulkin sun bukaci ECOWAS ta saka tsohon shugaban Nijar Issouhou Mahamadou a jerin mutanen da za'a tattauna da su a zaman sulhu da za'a yi a nan gaba.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Sojojin Juyin Mulin Nijar Sun Ce Wa’adin Rukon Kwaryarsu Ba Zai Wuce Shekaru Uku.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG