Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malaman Musulunci Sun Sake Kai Ziyarar Sulhu A Nijar


Sheikh Abdullahi Bala Lau lokacin da ya kai ziyarar sulhu Nijar tare da wasu malaman addinin Islama
Sheikh Abdullahi Bala Lau lokacin da ya kai ziyarar sulhu Nijar tare da wasu malaman addinin Islama

A karo na biyu a cikin kasa da mako biyu, wata tawagar Malaman addinin Islama daga Najeriya ta kai ziyaraa jamhuriyar Nijar a yammacinranar Laraba, inda suka gana da Shugaban sojojin da suka yi juyin mulki Janar Abdourahaman Tchiani da Firai Minista Ali Mahaman Lamine Zeine.

NIAMEY, NIGER - Wannan na zaman ci gaba da yunkurin warware rikicin siyasar da kasar ke fama da shi bayan kifar da gwamnatin zababben Shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.

Wasu daga cikin Malaman Addinin Islama da suka kai ziyarar sulhu Nijar
Wasu daga cikin Malaman Addinin Islama da suka kai ziyarar sulhu Nijar

A wata hira ta musamman da Muryar Amurka Jagoran tawagar Sheik Abdullahi Bala Lau, ya ce akwai alamun haske a kokarin sasanta bangarorin.

Daya daga cikin Malaman Addinin Islama da suka kai ziyarar sulhu Nijar
Daya daga cikin Malaman Addinin Islama da suka kai ziyarar sulhu Nijar

"Wannan ci gaba ne na kai da komowa a tsakanin Najeriya da Nijar, a matakin riga kafin hana shaidan samun rinjaye a rikicin siyasar da ya biyo bayan juyin mulkin da aka yi a wannan kasar" a cewar Sheik Bala Lau.

Ya kara da cewa Shugabanin kasashen nan biyu suna darajanta Malaman addinai, abin da ke nuni da alamomin nasarar da ke tattare da yunkurin da aka sa gaba. Saboda haka ya ce malamai za su ci gaba da addu’a domin neman mafita a wajen ubangiji.

Wasu daga cikin Malaman Addinin Islama da suka kai ziyarar sulhu Nijar
Wasu daga cikin Malaman Addinin Islama da suka kai ziyarar sulhu Nijar

"Kawo yanzu ana iya cewa Alhamdulillah addu’oin da ake yi sun sami karbuwa. Saboda haka lokaci ake jira kawai a ga komai ya warware cikin ruwan sanyi" a cewar Sheik Abdullahi Bala Lau Shugaban kungiyar Izalatul Bidi’ah wa Kimatus Sunnah na Najeriya, kuma shugaban tawagar Malaman Islama da ke shiga tsakani a dambarwar siyasar kasar jamhuriyar Nijar.

Saurari yadda hirar tasu ta kaya da Souley Moumouni Barma:

Wata Tawagar Malaman Addinin Islama Ta Sake Kai Ziyarar Neman Sulhu Nijar .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG