WASHINGTON, D.C. - Putin "ya jaddada mahimmancin warware matsalar cikin lumana don samun kwanciyar hankali a yankin Sahel," Goita ya ce a dandalin sada zumunta na X, wanda a da ake kira Twitter.
Kasashen yammacin duniya na fargabar cewa Nijar za ta iya fada wa irin halin da makwabciyarta Mali, wadda shugabanninta suka dauki hayar sojojin haya daga kungiyar Wagner ta Rasha domin taimaka musu wajen yakar ta da kayar baya, sakamakon hambarar da gwamnatin dimokaradiyya shekaru uku da suka wuce tare da korar sojojin Faransa.
Putin ya yi kira da a koma kan tsarin mulkin Nijar, yayin da shi kuma shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin ya yi maraba da juyin mulkin.
Da alama goyon bayan Rasha na karuwa a Nijar tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli, inda magoya bayan gwamnatin mulkin sojan kasar suka daga tutocin kasar Rasha a wasu taruka da dama.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna