Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Afrika Ta Dakatar Da Nijar, Sai An Maido Da Dokar Tsarin Mulki


Kungiyar hadin kan kasashen Afrika
Kungiyar hadin kan kasashen Afrika

Kungiyar hadin kan kasashen Afrika ta dakatar da Nijar daga duk wasu aikace aikacen da suka shafe ta da cibiyoyin ta, har sai an maido da ingantacciyar Dokar Tsarin mulki, sakamakon juyin mulkin da ya faru a watan jiya.

Kungiyar mai kasashe 55 ta tsaida kudurin ne bayan da wasu fadararrun sojoji suka kifar da gwamnatin shugaban da aka zaba ta tsarin Democradiyya, a watan jiya, suka gaggauta kame iko, da watsi da duk wata hanyar tattaunawa.

Shugaba Muhammed Bazoum da matar shi, da dansa suna karkashin daurin talala a gidansa dake Yamai babban birnin kasar.

Hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum
Hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum

Wannan dai shine karon farko da kungiyar ta yi Magana a fili tun bayan da ta zauna a baya domin tattauna batun rikicin na Nijar. Majalisar Kungiyar hadin kan kasashen na Afrika, ta yi kira ga dukan kasashe manbobin ta da sauran kasashen duniya, da su yi watsi da haramtacciyar gwamnatin kasar, da kaurace ma duk wani abu da ka iya ba haramtacciyar gwamnatin iko a doka.

An bukaci kungiyar hadin kan kasashen na Afrika AU, da kungiyar hadin kan Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS da su hanzarta mika jerin sunayen sojojin da suka yi juyin mulkin, da iyalan su da farar hula dake marawa sojojin baya, da suka hada da wadanda ke da hannu wajen keta hakkin Bazoum da sauran wadanda aka tsare tare da shi, domin aza musu takunkumi.

Shugabanin Kungiyar hadin kan kasashen Afrika
Shugabanin Kungiyar hadin kan kasashen Afrika

Mutanen dake kusa da Bazoum sunce an yanke mashi wutar lantarki da Ruwa, sannan abincin shi na gab da karewa.Kungiyoyin fafutuka sunce basu sami damar ganawa da Ministoci da ‘yan siyasar da sojojin juyin mulkin suka tsare ba.

Har ya zuwa wannan lokacin, kasashen yammaci na kallon Nijar a matsayin abokiyar hadin gwiwwa ta karshe a yankin Sahel dake kasa da sahara da za a iya aiki da ita wajen dakile ayyukan masu jihadi dake da alaka da Alqaida da kungiyar Islama. Kasashen Faransa da Amurka nada jami’an soji har 2500 a Kasar.

Ecowas da ta rika kokarin karya laggon jerin juyin mulki a ‘yan shekarun baya bayan nan, tayi barazanar yin amfani da karfi idan ba’a maida Bazoum bisa iko ba, amma wa’adin mayar da shi din yazo ya wuce ba tare da daukar wani mataki ba.

A karshen mako, wata tawagar ECOWAS ta je Yamai, amma jami’ai sun ce tattaunawar bata haifar da wani abin azo a gani ba, haka kuma sojojin sun cigaba da aiwatar da abin da suka tsara, cewa, zasu maida kasar bisa Dokar tsarin mulki cikin shekaru uku.

Kungiyar ta AU bata fayyace ko zata mara baya ga yin amfani da karfin soja ba.

Majalisar tsaro da zaman lafiya ta kungiyar ta AU na iya yanke hukunci akan batun yin amfani da karfin soja idan ta ga yuwuwar barazana ga zaman lafiyar mafi yawan yankin nahiyar.

Yayin da manbobin kungiyar ta ECOWAS suka amince da yin amfani da karfin soja domin maida Muhammed Bazoum bisa iko, kawuna na cigaba da kasancewa a rarrabe a kungiyar AU game da yin amfani da karfi.

~ Hauwa Sheriff~

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG