Labaran Maku Ya Zargi 'Yan Jarida da 'Yan Adawa da Azazzaba Matsalolin Tsaro

Labaran Maku, Ministan Watsa Labarai na Najeriya

Labaran Maku, Ministan Watsa Labarai na Najeriya

Bayan da majalisar zartaswa ta kasa ko FEC ta kammala taronta ministan yada labarai Labaran Maku ya fito fili ya zargi 'yan jarida da 'yan adawa da zazzaba matsalolin tsaro a kasar.
Majalisar ministoci ta kammala taronta jiya a Abuja inda suka tattauna muhimman abubuwan da suka shafi cigaban kasa da kuma matakan samar da zaman lafiya a duk fadin kasar.

Ministan watsa labaran kasar Mr. Labaran Maku ya fito fili ya zargi manema labaru da 'yan adawa da azazzaba matsaloli na tsaro a kasar da kuma dora kowane laifi akan shugaban kasa da gwamnatin Najeriya maimakon a ba kowane laifukan da suka taru a kansa domin a yi bincike.

Haka kuma Labaran Maku ya zargi masu zaman dirshen nan na yin zanga-zangar lumana domin a dawo da 'yan matan nan sama da dari biyu da aka sace a garin Chibok dake jihar Borno. Yace zaman dirshen dandali ne na 'yan adawa na jam'iyyun siyasa daban daban masu neman ci ma gwamnati mutunci. Labaran Maku yace idan aka duba wadanda ke yin zanga-zangar akan daliban Chibok fiye da kashi casa'in cikinsu 'yan adawa ne.

Dr Jibrin Ibrahim daya daga cikin shugabannin masu yin zaman dirshen kuma tsohon shugaban cibiyar gyara dimokradiya yace duk abun da Labaran Maku ke fada sheri ne kawai irin nasu. Duk wanda ya zo ya ga wadanda ke zaman dirshen sun san yawancinsu ma'aikatan gwamnati ne ko kuma mata da suke gida sai kuma mutane masu aiki daban daban. Babu 'yan siyasa cikinsu. Yace su sun ce gwamnati ta je ta bido yaran da aka sace amma kuma gwamnati bata son a fadi hakan. Yace jiya sun turo wasu da suka farfasa masu kujeru suka kwace masu wayoyi. Sun dauka zasu basu ji tsoro ne to amma suka ki su tsorata domin kasar tasu ce tare. Yansanda kuma na kallonsu. Sun barsu har suka gama abun da su ke son su yi. Amma masu zaman dirshen basu gudu ba.

A yanzu dai ga duka alamu irin matakan da gwamnati ke dauka domin tarwatsa gangamin na neman ya kawo takunsaka tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyi daban daban wadanda suna ganin gwamnati ta fara ajiye dimokradiya gefe daya tana dosan soma mulkin kamakarya.

Ga rahoton Umar Faruk Musa.

Your browser doesn’t support HTML5

Labaran Maku Ya Zargi 'Yan Jarida da 'Yan Adawa da Azazzaba Matsalolin Tsaro - 3'35"