Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mazauna Chibok Na Takaicin Matakin Kwamitin Shugaban Kasa


Mutane a wurin zanga-zangar kira ga gwamnati da ta kubuto da mata ‘yan makaranta da aka sace a Chibok, a Maiduguri, alhamis 22, ga Mayu 2014.
Mutane a wurin zanga-zangar kira ga gwamnati da ta kubuto da mata ‘yan makaranta da aka sace a Chibok, a Maiduguri, alhamis 22, ga Mayu 2014.

Daya daga cikin shuwagabannin Kungiyar Dattawan Chibok a Jihar Borno dake Najeriya, yace kwamitin da shugaban kasa ya kafa saboda daliban da aka sace ya gaza haduwa da kungiyar, da kuma kai ziyara Chibok duk da cewa kwamitin yayi alkawarin yin haka.

Mallam Shettima Dunoma yace dattawan Chibok suna shirya gudanar da zanga-zangogi a duk fadin garin Chibok din, domin matsawa gwamnatin Shugaba Jonathan lamba wajen gani an mayar da daliban wajen iyayensu.

Ya kara da cewa dattawan suna so suji tanadin da kwamitin yake yi akan neman daliban.

“Muna nan gida, kuma duk wanda yace mana zai zo, tu muna nan muna jira mu gani ko zasu dawo mana da yaranmu,” inji Dunoma. “Saboda haka, duk wata kungiya da tace zata zo Chibok, muna kagara mu hadu da ita, ko muji me zata ce mana, ko wata kila su dawo mana da dalibanmu.”

Rahotanni sun tabbatar cewa mambobin kwamitin da shugaban kasa ya nada dangane da Chibok, sun riga sun shiga jiragen sama sun koma Abuja, ba tare da zuwa Chibok. Rahoton yace wata kila kwamitin ya gagara zuwa Chibok ne saboda dalilan tsaro.

Dunoma yace mazauna Chibok na gani kamar gwamnati dake Abuja tayi watsi da su ne.

“Muna matukar takaici, wasu daga cikinmu na tunanin kamar ba’a damu da bangarenmu ba, a wannan kasa,” inji Dunoma. “Saboda wannan sace dalibai da aka yi, ba’a taba yi a ko ina ba a Najeriya, saboda haka meyasa sai daliban Chibok? Meyasa? Saboda ba’a damu da mu ba.

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG