Kakakin Maikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki, ta fada jiya talata cewa, ko da Amurka ta san inda suke, ba zata fito fili ta bayyana ba.
Haka kuma kamar yadda hukumomin Najeriya suka fadi, ita ma Amurkan watakil ba zata yi garajen daukan matakan kubutar da su ba saboda tsaron lafiyar ‘yan matan.
A cikin watan jiya ne kungiyar ta Boko Haram ta sace kimanin yara ‘yan makaranta su kusan dari uku a Chibok cikin jihar Borno.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce gwamnatins a ba zata tattauna da ‘yan kungiyar ba, daga nan ta bukaci a sako sub a tareda wani sharadi ba.
Wani jami’I a yankin Chibok ya gayawa wani ma’aikacin VOA cewa shugaban kasa ya amince da bukatar kungiyar Boko Haram na ganin an saki ‘yan kungiyar da gwamnati take tsare dasu, su kuma su saki ‘yan matan.