Wani Emmanuel Yagani mahaifin Naomi Emmanuel Yagani daya daga cikin daliban da aka sace yace gaf da aukuwar lamarin sun tafi makarantar inda suka ga rigunan daliban zube a kasa kuma an kone yawancin gine-ginen makarantar.
Washegari sun fita har sun kai Damboa inda suka ga an tara 'yan matan a karkashin itacen dorawa. Shugaban hukumar Chibok ya kawo sojoji cikin motoci uku domin a bi sawun yaran. Bayan da sojojin suka yi gaba kadan sai suka ce basu da makaman da zasu tunkari 'yan Boko Haram din.
Bayan kwana biyu su iyaye sun hada kansu sun tafi dajin amma wani dan taliki ya fada masu inda daliban suke amma ya yi masu kashedi kada su tunkaresu domin dukansu zasu halaka.
Bayan mako daya an sake kawo sojoji akan wai iyayen su tafi da sojojin. Amma daga bisani an fada masu kada su je domin sojojin dake dajin ba zasu iya tantancesu ba daga 'yan Boko Haram.
Dangane da cewa gwamnati ta tura sojoji su yi kokarin kubutar da yaran sai Emmanuel yace babu wani kokari da sojojin ke yi. Ga su iyaye babu abun da ya sake. Misalli yace ranar da aka ce kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa zai ziyarcesu sai wani ya zo yace 'yan Boko Haram na zuwa sai suka gudu kana 'yan kwamitin suka soke zuwansu. Sojoji ma sun gudu. Wasu sun buya a jikin katanga, wasu kuma a cikin bahaya.
Iyayen suna ganin alkawarin da aka yi masu cewa za'a kubutar da 'ya'yansu zolaya ce kawai. Basa ganin sojoji zasu iya kubutar da 'ya'yansu daga hannun Boko Haram. A ganinsu karya a ke shirya masu.