Gwamnan yayi jawabinsa ne ga 'yan kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Sokoto da suka gudanar da zanga -zangar lumana ta nuna alhini da bacin rai akan kasa gano daliban har tsawon makonni biyar. Masu zanga-zangar sun yi maci ne zuwa fadar gwamnan.
A jawabinsa yace na farko kowa yayi addu'a Allah Ya kawo daliban lami lafiya ga iyayensu. Yace kada Allah Ya sa a cutar da su yayin da suke hannun 'yan Boko Haram din. Yace abun ya riga ya faru. Haka Allah Ya kaddara zai faru ta hannun miyagun mutane da suke kiran kansu Boko Haram. Yayi addu'ar Allah Ya tonasu Ya kuma karyasu ya kuma kare na gaba. Yace halin da ake ciki ba hali ba ne na raba laifi, wato a ce ga mai laifi ga mara laifi. Kamata yayi a hada kai a ceto yaran. Yace duk wata magana da ba haka ba bata da wani anfani.
Shugaban kungiyar malaman reshen Sokoto Cika Maidamma Alkamawa yace bayan daliban da aka sace suna kuma jajantawa akan malamai fiye da 170 da aka kashe a rikicin na Boko Haram tsakanin jihohin Borno da Yobe. Abun da ya dada bata masu rai shi ne yadda gwamnati tayi biris da abubuwan da suka faru.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.