Kakakin rundunar tsaro da ake kira SPECIAL TASK FORCE dake Jos fadar gwamnatin jihar Filato Keften Ikedichi Iweha ya tabbatar da aukuwar lamarin ya kuma ce sun kara tura jami'an tsaro a wurin.
Yace kwantar bauna aka yiwa sojojinsu dake sintiri a kauyen lamarin da yayi sanadiyar mutuwar sojoji hudu. Yace dama can garin na fama da hayaniyar rashin zaman lafiya tsakanin mutanen garin da wasu da ba'a tantance ba. Yace dalili ke nan da aka tura sojoji kauyen domin a karfafa tsaro a kuma kare mazauna garin. Yanzu babu matsala kuma bincike na cigaba.
Shugaban karamar hukumar Mr. Nanchual Bendel Lofa yace 'yan bindiga sun saba shiga karamar hukumar ta yankin inda lamarin ya faru. An sha yin kone-kone da kashe-kashe a yankin da kone dukiyoyin mutane kusan har sau biyar. Dalilin haka ne aka tura sojoji yankin. Yace mutanen dake yankin manoma ne amma Fulani basa son manoman su zauna a yankin domin su dinga kiwo da shanunsu.
To saidai Fulani sun ce shekaru da dama babu Fulani a yankin. Shi shugaban karamar hukumar yace gaskiya da suna zaune da Fulani sai wata rana suka ga Fulanin suna tashi da daddare. Wanshekare suka dawo suna kone-kone da kashe-kashe mutanen yankin.
Yanzu dai an je wurin da lamarin ya faru an rokesu da su yi hakuri da abun da ya faru. Shi ma sakataren kudi na kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Filato kuma shugaban kungiyar a karamar hukumar Shendam Alhaji Salihu ya roki jami'an tsaro da su yi kyakyawan bincike kafin su yanke hukunci. Yace idan jami'an tsaro basu manta ba a wurin aka kashe shanu fiye da arba'in lamarin da ya sa Fulanin suka tashi.
Ga rahoton Zainab Babaji.