Kaka Lawan yace kishin kasa da tabbatar da ceto garinsu yasa 'yan goran suka tashi tsaye musamman a cikin Maiduguri. Su ne suka bi kwararo-kwararo suna kama 'yan kungiyar Boko Haram domin sun sansu. Dalili ke nan yau ana iya tafiya cikin walwala a cikin garin na Maiduguri.
A kokarn shigo da su 'yan Civilian JTF cikin shirin tsaro Shehu Lawan yace sun yi shirin tallafawa matasan da goyon baya saboda su samu su yi aikin da su keyi a sawake. Shirin ya hada da basu tallafi domin jin dadain rayuwa.
Gwamnati ta raba 'yan goran kashi biyu. Na farko da ya kunshi mutane 678 cikin mutane 800 da suka bukata. A karo na biyu sun nemi mutane dubu daya amma sun samu fiye da haka saboda yadda aka tafiyar da shirin horo na fari. Karo na biyun ya hada ma har da mata. Yanzu sun kammala shirin horas da rukuni na uku. Da tuni sun fara na ukun idan ba wata matsala da suka samu ba. Amma yanzu sun shawo kan matsalar. Kwanan nan zasu dauki mutane dubu daya su basu horo na mako uku.
Dangane da irin horon da suke basu Kaka Lawan yace ana basu horo irin na soja. Babu wani banbanci. Ita kuma gwamnatin jiha tana biyansu dan alawus kana ofishin shi kwamishanan shari'a yana aiki akan dokar da zata kafa masu tushen yin aikin. Gwamnati ta raba Maiduguri goma ta raba masu ta kuma saya masu motoci 21. Suna da rigunan aiki da usur. Suna aiki tare da sojoji. Kowane wata ana basu tallafi. Shugabannin kananan hukumomi kuma suna tallafa masu kowane wata. Duk wanda yake da kuzarin shiga soja gwamnati zata tallafa masa ya shiga aikin sojan yayin da sojoji suka soma daukan sabbin kurata.
Ga karin bayani.