Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jonathan Na Son Jawabi Akan Kasa a Coci


Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan

Wasu 'Yan Najeriya na Korafin Akan Jawaban Shugaban Kasa a Coci.

A Najeriya ga dukan alamu Shugaba Goodluck Jonathan bai fara sauraren masu sukar sa ba a cewar yana bayanai da suka shafi kasa, a duk lokacin da yaje aiki na ibada, a Coci.

Bayanai na baya-bayan nan da shugaban yayi a Coci ranar lahadi ya nuna cewa shekaru uku basu isa a tabbatar da aiyuka na gwamnati ba sanan kuma matsalla ta Boko Haram,matsalla ce da take bunkasa domin a kada gwamnatin sa.

Akan haka ne wadansu malaman addini suka yi musayan ra’ayi dagane da hakan inda Shiekh Hussaini Zakariya,wani malamin addinin Islam a Abuja yake ganin cewar bai kamata shugaba Jonathan ya rika hada addini da sha’ani na siyasar sa ba,yace “ abunda kundin tsarin milkin Najeriya,ya tabbatar shine addini da ban kuma siyasa daban,wato kennan ba’a gauraya siyasa da addini,idan shugaban kasa musulmi yaje masalaci,shugaba a masalacin shine Liman,abunda liman yayi shi zai yi a musulunci ko lokaci ba’a bashi yayi Magana akan wani abu wanda ya shafi kasa ko kuma ya shafeshi mulkinsa ,iyakaci ayin sallah kwai ya tafi.”


Ya kara da cewa “haka kuma idan kirista ne yakamata idan ya tafi wajen Coci abunda akeyi na ibada shi zai yi da adu’oinsu shi kennan kowa ya waste,amma ace shugaba, ba zai yi wata Magana mahimiya ba inda ya dace lokacin taron Ministoci na mako-mako ko lokaci taron shi da ‘yan jarida na wata-wata saidai kowace lahadi aji wani abu mahimmi ya fito daga coci,to wannan yakamata shuwagabanin cocin nan da malamansu,su gayamasa kada ya gubatamasu ibada da siyasa.”

Shi kuma Rev. Sabo Yaro Adams, cewa yayi ”shugaban kasa duk inda akwai taron jama’a so da dama akan gayace shi domin aji shirye-shiryen shi game da mulkin kasa wannan bai sabawa kaidan addini ba.”

A halin da ake ciki dai babu alama cewa lallai shugaba Goodluck Jonathan zai dena jawaban nan da yakeyi a cikin coci duk kuwa da korafin da wasu ‘yan kasar sukeyi ganin irin tasirin da yanzu addini yakeyi akan sha’ani na syasa a cikin Najeriya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:24 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG