Kungiyar AU Ta Dakatar  Da Gabon Daga Kungiyar Bayan Juyin Mulkin Sojoji

Shugabannin kasashen cikin kungiyar Tarayyar Afirka a wurin taron

A ranar Alhamis kungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta dakatar da Gabon daga zama mambar kungiyar, kwana guda bayan hambarar da shugaban kasar Ali Bongo.

Wannan dai shi ne matakin farko na yanki da kungiyar ta dauka a matsayin mayar da martani ga juyin mulki karo na takwas da aka yi a yammaci da tsakiyar Afirka tun shekarar 2020.

Juyin mulkin dai ya kawo karshen mulkin daular Bongo na kusan shekaru sittin ya kuma haifar da wani sabon rikici a yankin da ya fuskanci guguwar juyin mulki.

Hambararen Shugaban Gabon, Ali Bongo

Kamar sauran gwamnatocin mulkin soja da suka kwace mulki a yankin, shugabannin sojojin Gabon na neman karfafa mulki duk da Allah wadai da kasashen duniya suka yi.

Ana sa ran za a rantsar da Janar Brice Oligui Nguema a ranar Litinin, wanda shi ne jagoran juyin mulkin kuma tsohon shugaban dakarun tsaron fadar shugaban kasar.

Kanar Brice Nguema

Tinubu, wanda ke jagorantar kungiyar raya tattalin arzikin yankin yammacin Afrika ta ECOWAS, ya fada ranar Alhamis cewa "fargabasa ya tabbata a Gabon, wato fara samun masu koyi da wannan lamarin."

Kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar Tarayyar Afirka ya dauki mataki na farko a ranar Alhamis ta hanyar hana kasar Gabon shiga dukkan ayyukan kungiyar da cibiyoyinta har sai an dawo da tsarin mulkin dimokradiyya a kasar.

Ita ma kungiyar siyasar Afirka ta tsakiya, wadda Gabon ta kasance mamba, ta yi Allah wadai da juyin mulkin a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta kuma ce zata shirya wani taro na shugabannin kasashe domin sanin yadda za su mayar da martani. Sai dai bata fadi lokaci ba.

Kafin wayewar garin ranar Laraba ne dai manyan hafsoshin sojan kasar Gabon suka sanar da yin juyin mulki, jim kadan bayan da hukumar zaben kasar ta bayyana cewa Bongo ya samu nasara karo na uku a zaben da aka gudanar a ranar Asabar.

Daga baya a ranar Laraba, wani bidiyo ya nuna Bongo a tsare a gidansa, yana neman taimako daga kasashen duniya, amma da alama bai san abin da ke faruwa a kusa da shi ba.

Babban dandalin 'yan adawar Gabon, Alternance 2023, ya godewa gwamnatin mulkin sojan kasar a ranar Alhamis kan kawo karshen mulkin Bongo na tsawon shekaru.

Abubuwan da ke faruwa a Gabon na zuwa ne bayan juyin mulkin da aka gani a baya-bayan nan a Mali, Guinea, Burkina Faso, Chadi da Nijar. Juyin mulkin ya kuma nuna gazawar manyan kasashen Afirka wajen daukar kwakkwaran mataki da zarar sojoji suka karbe ragamar mulkin kasa.

Kungiyar ECOWAS ta yi barazanar amfani da karfin soja a Nijar bayan juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli da kuma sanya takunkumi, amma gwamnatin mulkin sojan kasar ba ta ja da baya ba. Shugabannin soji a wasu wurare ma sun yi tir da matsin lamba daga kasashe a kan maido da mulkin farar hula.