Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin Tsaron Kasashen Nahiyar Turai Za Su Yi Taron Gaggawa Kan Juyin Mulki A Gabon


Joseph Borrell
Joseph Borrell

Ministocin tsaron kasashen nahiyar Tarayyar Turai za su tattauna halin da ake ciki a Gabon, in ji kungiyar EU.

WASHINGTON, D.C. - Wasu manyan hafsoshin sojin kasar Gabon sun bayyana a gidan talabijin na kasar da sanyin safiyar Larabar nan, inda suka ce sun karbi mulki.

AFR-GEN GABÓN - Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Gabon
AFR-GEN GABÓN - Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Gabon

Matakin sojin na zuwa ne sa’o’i bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da cewa Shugaba Ali Bongo ya sake lashe zabe a karo na uku.

Babban jami’in kula da harkokin wajen kungiyar EU, Josep Borrell ya bayyana haka ne a ranar Laraba 30 ga watan Agusta, inda ya kara da cewa juyin mulkin idan har aka tabbatar da hakan zai kara haifar da rashin zaman lafiya a yankin.

"Duba, wannan yanki gaba daya, tun daga Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, sannan Mali, sannan Burkina Faso, yanzu ga Nijar, watakila Gabon, yana cikin wani mawuyacin hali.

“Kuma tabbas yau ministocin tsaro da na harkokin waje dole ne mu yi tunani mai zurfi game da abin da ke faruwa a can da kuma yadda za mu inganta manufofinmu game da waɗannan kasashe. Wannan babban batu ne ga Turai" in ji Borrell.

EU: Josep Borrell
EU: Josep Borrell

Kawo yanzu dai babu wani karin haske daga gwamnatin kasar wadda mamba ce a kungiyar OPEC.

Har ila yau, babu cikakken bayani kan inda Bongo yake, wanda aka gani na karshe a bainar jama'a lokacin da ya kada kuri'arsa a zaben ranar Asabar 26 ga watan Agusta.

Idan dai har aka yi nasara, juyin mulkin zai zamana karo na takwas a Yammacin Afirka da Tsakiyar Afirka tun daga shekarar 2020.

Karbe mulkin da aka yi a Mali, Guinea, Burkina Faso, Chadi da Nijar ya kawo cikas ga ci gaban dimokradiyya a 'yan shekarun nan.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG