Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashen Afirka Za Su Fara Tattaunawa Akan Juyin Mulkin Gabon


Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS/CEDEAO (Hoto: Facebook/CEDEAO/ECOWAS)
Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS/CEDEAO (Hoto: Facebook/CEDEAO/ECOWAS)

Shugabannin kasashen Afirka sun fara tattaunawa game da martanin da za su yi ga jami’an kasar Gabon da suka hambarar da shugaba Ali Bongo tare da nada nasu shugaban, wanda shi ne na baya bayan nan a jerin juyin mulki a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka da manyan kasashen yankin suka kasa magancewa

WASHINGTON, D.C. - Kwace mulkin dai ya kawo karshen daular iyalin Bongo na kusan shekaru sittin da ta yi tana mulki tare da haifar da wata sabuwar dambarwa ga shugabannin kasashen yankin da suka yi ta fafutukar ganin an samu ingantaccen martani ga juyin mulki takwas da aka yi a yankin tun daga shekara ta 2020.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afrika ta ECCAS, ta yi Allah wadai da juyin mulkin a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce ta shirya wani taron "na gaggawa" na shugabannin kasashen domin sanin yadda za'a mayar da martani. Amma basu sa rana ba.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, kuma shugaban kungiyar ECOWAS na yammacin Afirka a ranar Laraba, ya ce yana aiki kafada-da-kafada da sauran shugabannin Afirka domin dakile abin da ya kira "mulkin kama karya" da ke yaduwa a fadin Afirka.

AFR-GEN GABÓN - Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon
AFR-GEN GABÓN - Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon

Manyan hafsoshin soji a Gabon sun sanar da juyin mulkin kafin wayewar garin ranar Laraba, jim kadan bayan da hukumar zabe ta bayyana cewa Bongo ya sami nasarar lashe zabe a wa'adin mulki na uku bayan zaben ranar Assabar da ta gabata.

Daga bisani a ranar Laraba, wani faifan bidiyo ya bayyana na Bongo da ake tsare da shi a gidansa, yana neman taimako daga kasashen duniya, amma da alama bai san abin da ke faruwa da shi ba. Jami’an sun kuma sanar da cewa an zabi Janar Brice Oligui Nguema, tsohon shugaban rundunar tsaron fadar shugaban kasa a matsayin shugaban kasa na yanzu.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Abubuwan da suka faru sun biyo bayan juyin mulkin shekaru hudu da suka gabata a Mali, Guinea, Burkina Faso, Chadi da Nijar, tare da kawar da tsarin dimokuradiyya tun a shekarun 1990, wanda ya kara haifar da damuwa a tsakanin kasashen ketare da ke da muradu a yankin. Juyin mulkin ya kuma nuna gazawar manyan kasashen Afirka da zarar sojoji suka karbe ragamar mulkin kasar.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG