YAOUNDÉ, CAMEROON - Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba yana "tsare a gida" da iyalansa da likitocinsa da suka kewaye shi.
Rahotanni sun ce an kama daya daga cikin 'ya'yansa bisa laifin cin amanar kasa, kamar yadda sojoji suka sanar.
“Muna sanar da al’umar Gabon da fadin duniya baki daya cewar Ali Bongo da iyalansa suna tsare a gida, tare da likitotinsa.
"Wadannan mutane da za mu kira sunayensu, za mu mika su gaban shari’a a bisa laifin cin amanar kasa, cin hanci da rashawa, amfani da tambarin Shugaban kasa ba bisa ka’ida ba, dillacin miyagun kwayoyi. Sunayen sun hada da Nourredine Bongo Valentin, Yan Ghislain Ngoulou, Mohamed Ali Saliou, Abdoul Ousseini, Jessy Ella Ekoga, Stive Djeko da Cyriac Gourandjan" in ji Kakakin sojojin.
Ali Bongo da kansa ya bayyana cikin wani bidiyo da aka yada a yanar gizo inda ya tabbatar da cewar “Ina sanar da jama’a baki daya cewa sojoji sun tsare ni a nan gida na. Ban san halin da muke ciki ba. Ku fito gaba daya ku tona asirin su. Ina kuma neman taimakon abokan arziki a fadin duniya domin mu samu mafita dangane da wannan al’amari.”
Abin mamaki anan shi ne farin ciki da mafi yawancin al’umar kasar suka nuna kan wannan juyin mulki musamman Noe Ndinga Shugaban wata kungiyar malaman makaranta.
Ndinga ya ce ”babu shakka a yadda kasar take tafiya, alamu sun nuna za’a kai wannan mataki. Da duk kokari da Ali Bongo yayi wajen habaka tattalin arzikin kasarmu, mun san ba shi da koshin lafiya. Yanzu fatar mu ita ce sojoji su sanar da mu manufar su bayan sun kawar da gwamnatin Bongo”.
Daruruwan sojoji sun fito kan titi suna kirarin sunan Janar Brice Oligui Nguema, Shugaban rundunar tsaro (GR), mai gadin hambararren Shugaban kasar Ali Bongo Ondimba, wanda shi ne ake ganin zai maye gurbin Shugaba Bongo.
Saurari cikakken rahoto daga Mohamed Bashir Ladan:
Dandalin Mu Tattauna