WASHINGTON, D.C - Jami’an soji a kasar Gabon mai arzikin man fetur sun ce sun kwace mulki a ranar Laraba 30 da watan Agusta.
Sun kuma sanar da tsare Shugaba Ali Bongo, bayan da hukumar zaben kasar da ke tsakiyar Afirka ta sanar da cewa ya sake lashe wa’adi na uku.
A ranar Asabar aka gudanar da zaben shugaban kasa a kasar wanda sakamakonsa ke cike da korafe-korafe.
A cikin sanarwar da aka yi ta gidan talabijin da tsakar dare, wasu manyan jami’an soji 12 sun bayyana cewa an soke sakamakon zaben.
Sojojin sun kuma sanar da rufe kan iyakokin kasar da kuma rusa duk wasu cibiyoyin gwamnati.
Shugabannin juyin mulkin sun ce sun dauki wannan mataki ne da yawun dukkan hukumomin tsaron kasar.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna