Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kwace Mulki A Gabon


Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon
Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon

Juyin mulkin na zuwa ne 'yan sa'o'i kadan bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da Shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi.

Wasu sojojin kasar Gabon sun sanar da hambarar da shugaba Ali Bongo.

Wannan dai na zuwa ne jim kadan bayan nasarar da ya samu a zaben na ranar Asabar, wanda ‘yan adawa ke da dumbin korafe-korafe akan yadda zaben ya gudana.

Sojoji sun yi ta yada zango a gidan talabijin na kasar Gabon don ayyana kwace iko da suka yi a kasar.

Shugabannin juyin mulkin sun kuma bayar da sanarwar soke sakamakon zaben da ya gaduna ranar Asabar 26 ga watan Agustan 2023.

A birnin Libreville, jama'a sun dunguma kan tituna suna nuna farin cikinsu a cewar AP, inda aka ga suna ta rera taken kasar.

Shugaban Gabon, Ali Bongo (AFP0
Shugaban Gabon, Ali Bongo (AFP0

Shugaba Ali Bongo mai shekaru 64, wanda ya hau karagar mulki a shekara ta 2009 bayan rasuwar mahaifinsa, ya sake tsayawa takara karo na uku a zaben da aka yi ta fama da rigingimun.

Shekara 55 iyalan Bongo suka kwashe suna mulkar kasar ta Gabon.

Gabon ita ce kasa ta biyar da Faransa ta rena da sojoji suka yi juyin mulki a baya-bayan nan.

Juyin mulkin na Gabon na zuwa ne wata guda bayan da sojoji suka kifar da gwamantin Shugaba Mohamed Bazoum a Jamhuriyar Nijar.

Kungiyar kasashen yammcin Afirka ta ECOWAS ta yi Allah wadai da lamarin inda take ta kokarin ganin ta maido da mulki hannun farar hula.

Yadda al'umar kasar ta Gabon ke murna bayan juyin mulki (Reuters)
Yadda al'umar kasar ta Gabon ke murna bayan juyin mulki (Reuters)

Daga cikin matakan da ta ce za ta dauka har da amfani da karfin soji yayin da duk wani yunkuri na samar da maslaha ya citura.

Har zuwa lokacin bayar da wannan rahoto, babu tabbas kan martanin da kasashen duniya za su mayar dangane da wannan al’amari.

Kungiyoyi kamar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS da kungiyar tarayyar Afrika AU da suka yi kakkausar suka ga juyin mulkin da aka yi a Nijar, ba su fitar da wata sanarwa dangane da rikicin kasar Gabon ba a yanzu haka.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG