WASHINGTON, D. C. - Bayan shekaru uku an hambarar da shi a wani juyin mulki, kafin daga bisani aka mayar da shi kan karagar mulki bayan da Faransa ta shiga tsakani.
- 1967: Lokacin Da Iyalan Bongo Suka Karbi Mulki --
M'Ba ya rasu a shekara ta 1967 kuma mataimakinsa Albert-Bernard Bongo ya gaje shi. Bongo ya kafa kasa mai jam’iyya daya kacal, inda ya yi mulki ta hanyar amfani da tsauraran matakai tare da amfana da arzikin man kasar.
Ya musulunta a shekarar 1973, inda ya canza sunansa zuwa Omar Bongo. A matsayinsa na ‘dan takara daya tilo, an zabe shi a matsayin shugaban kasa a 1973, 1979 da 1986. Bayan nan aka bullo da tsarin jam'iyyu da yawa bayan tashe-tashen hankula da tarzoma a 1990 amma duk da haka Bongo ya lashe zabe a 1993, 1998 da 2005.
- 2009: Mulki Ya Koma Hannun ‘Dan Bongo -
Bongo ya mutu ne a watan Yunin 2009, bayan zaben da aka yi ta ce ce-ku-ce a watan Agusta, daga bisani aka rantsar da daya daga cikin 'ya'yansa Ali Bongo a watan Oktoba a matsayin shugaban kasa. Duk da kalubalen da aka fuskanta, lamarin da ya kai mummunan tashin hankali. 'Yan adawa sun yi ta Allah wadai da tsarin mulkin Bongo.
A shekara ta 2010 masu shigar da kara na Faransa suka bude wani bincike kan kadarorin Bongo ya mallaka a Faransa da wasu Shugabannin kasashen Afirka.
- 2014: Barkewar Rikici A Gabon -
A shekara ta 2014 ne rikici ya barke tsakanin magoya bayan ‘yan adawa da jami’an tsaro a lokacin da aka haramta zanga-zangar neman Bongo ya sauka a mulki.
- 2016: Rikici Bayan Zabe -
An gudanar da zaben na 2016 cikin yanayi na fargarba. Gwamnati a lokacin ta yi ta fama da mtsalolin yaje-yajen aiki, kasafin kudi da kuma faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya. Jean Ping, shi ne babban abokin hamayyar, wanda tsohon jami’in diflomasiyya ne da ya jagoranci kungiyar tarayyar Afirka ta AU ya kuma rike manyan mukamai a Majalisar Dinkin Duniya.
A lokacin da hukumar zaben kasar ta sanar da cewa Bongo ya yi nasara, sai wani kazamin rikici ya barke bayan zaben.
- 2018: Cutar Bugun Jini -
Bongo ya yi fama da matsalar bugun jini a watan Oktoban 2018 yayin da yake Saudiyya. An dauke shi zuwa Maroko inda ya kwashe lokaci mai tsawo yana jinya
- 2019: Juyin Mulkin Da Bai Yi Nasara Ba -
A ranar 7 ga watan Janairun 2019 ne sojoji masu tayar da kayar baya suka yi yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba, ganin cewa Bongo ba ya cikin kasar.
- 2022: An Tuhumi Yaran Bongo Tara -
Daga Maris zuwa Yulin 2022, masu shigar da kara na Faransa suka tuhumi ‘ya’yan Omar Bongo tara da laifin almundahana, ciki har da almubazzaranci da dukiyar jama’a da mallakar kadarori a Faransa.
Masu shigara da karar, sun yi da'awar cewa dangin na rike da kadarorin da aka kiyasta kudinsu zai kai kimanin Euro miliyan 85 a Faransa.
- 2023: Sabon Tsarin Mulki -
A watan Afrilun 2023, Majalisar Dokokin Gabon ta kada kuri'ar yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar tare da rage wa'adin shugaban kasa daga shekaru bakwai zuwa biyar. Sassan 'yan adawa sun soki sauye-sauyen da aka samu, musamman karshen zagaye na biyu na kada kuri'a, a matsayin hanyar "samun sake zaben" Bongo.
- 2023: Juyin Mulkin Bayan Zabe -
Jami’an soji sun fada a ranar Laraba cewa sun kifar da gwamnati a wani gagarumin juyin mulki bayan da aka bayyana cewa Shugaba Ali Bongo ya lashe zaben da aka gudanar da kashi 64.27 na kuri’un da aka kada.
A yanzu sojojin da suka yi juyin mulki suna tsare da shi a cikin gida.
-Agence France-Presse K/amfanin Dillancin Labaran Faransa
Dandalin Mu Tattauna