Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nahiyar Afirka Ta Fuskanci Juyin Mulki Har Sau Takwas Cikin Shekaru Uku


Juyin mulki a Nahiyar Afirka
Juyin mulki a Nahiyar Afirka

A shekarar 2021, sojoji sun kaddamar da juyin mulki a kasar Mali, bayan da hambarar da zababbiyar  gwamnatin demokradiyya ta Ibrahim Boubacar Keita a 2021 tare da nada gwamnatin rikon kwarya, Bah Ndau, wani matashin hafsan soja dan kimanin shekaru 43.

Kanar Assimi Goita ya hambaras da gwamnatin Ndau.

Shi kansa shugaban sojojin juyin mulkin, Kanar Goita ya tsallake rijiya da baya bayan da akai yunkurin halaka shi yayin da yake sallar jummu'a a wani masallaci da ke Bamako, babban birnin kasar.

A Kasar Guinea, nanma wani matashin soja dan kimanin shekaru 43, Kanar Mamadi Dambouya ya jagoranci juyin mulkin da ya hambaras da gwamnatin demokradiyya ta shugaba Alpha Conde.

Kanar Mamadi Dambouya
Kanar Mamadi Dambouya

Ranar ashirin da biyar ga watan Oktoban 2021, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Sudan, Laftanar Janaral Abdel Fatah Alburhan ya hambaras da gwamnatin rikon kwarya da ke karkashin jagorancin Abdallah Hamdok.

Bayan dai kokawar neman mulki, mummunan rikici ya barke tsakanin Janar Alburhan da mataimakinsa Janar Mohammed Daglo, rikicin da a halin yanzu ke ci gaba da tarwatsa kasar ta sudan da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu biyar cikin wata biyar.

Janar Alburhan
Janar Alburhan

A Burkina Faso, wani matashin hafsan soja dan kimanin shekaru 34, Laftanar kanar Ibrahim Traore ya fatattaki gwamnatin demokradiyya ta shugaba Henry Sandaogo Damiba a watan satumban bara, Kanar Traore dai a halin yanzu shine shugaban kasa mafi karancin shekaru a duk duniya.

Kanar Ibrahim Traore
Kanar Ibrahim Traore

A karshen watan jiya ne kuma kwamandan askarawan da ke tsaron fadar shugaban kasa a Nijar karkashin jagorancin Janar Abdourrahmane Tchiany su ka hambaras da shugaba Bazoum Muhammad.

Janar Abdouramane Tchiani
Janar Abdouramane Tchiani

A wani abu mai kama da arashi kuma, suma sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasa a Gabon karkashin jagorancin Kanar Brice Clotaire Oligui Nguema ya jagoranci juyin mulkin da ya hambaras da Shugaba Ali Bongo.

Kanar Brice Nguema
Kanar Brice Nguema

Kwararre kan kimiyyar siyasa Dr. Sa'idu Ahmad Dukawa na cewa tsananin rayuwa da matsalar tattalin arziki da magudin zabe da dadewar shugabanni a kan mulki na daga cikin dalilan da ke jawo yawan juyin mulkinnan.

Saurari cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG