JAMHURIYAR NIJAR: Gwamnan Jihar Maradi Ya Saki Wasu 'Yan Kaso Ba Bisa Kan Ka'ida Ba

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

A wani taron manema labarai da kungiyar alkalan shari'a reshen jihar Maradi tayi ta zargi gwamnan jihar da sakin wasu 'yan kaso ba bisa kan ka'ida ba.

Kungiyar tayi tur da Allah wadai da sakin wasu 'yan kaso ba cikin ka'ida ba da gwamnan jihar yayi saboda ya yi masu katsa ladan.

Malam Rura Abdullahi magatakardan alkalan yace an samu cewa mutane uku an samesu da laifi kuma jami'an tsaro sun yi aikinsu. An gurfanar dasu gaban shari'a kuma an tsaresu a gidan kaso a Damagaran. Amma a cikin dare gwamnan ya umurci masu tsaron gidan kason su sakesu.

To alkalan jihar sun yi tur da katsa landan da gwamnan yayi cikin harkokin shari'a. Muryar Amurka tayi kokarin jin ta bakin gwamnan jihar amma kokarin yin hakan ya cutura.

Saidai kungiyar alkalan ta yi kira ga shugaban kasa da sauran takwarorinta su dauki matakan magance irin wannan katsa landan. Magatakardan kungiyar alkalan yace rajistra din gidajen shari'a zai kama gwamnan jihar domin wadanda gwamnan ya fitar 'yan kasar Nijar ne kamar kowa. Basu fi kowa ba. Shugaban kasa shi ne shugaban shari'ar kasa saboda haka wajibi ne ya dauki mataki.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

JAMHURIYAR NIJAR: Gwamnan Jihar Maradi Ya Saki Wasu 'Yan Kaso Ba Bisa Kan Ka'ida Ba - 2' 45"